An ga watan Shawwal, gobe take Sallah

0

Majalisar koli ta addinin Musulunci, NSCIA, ta sanar da ganin watan Shawwal a garin Damaturu, jihar Yobe.

Shugaban majalaisar, Ishaq Oloyode ne ya sanar da haka inda yace sarkin Musulmi, Dr Sa’ad Abubakar zai yi sanarwa a cikin daren Litinin.

Gobe Talata ne za a yi sallar Eid-el Fitr a Najeriya da wasu kasashen duniya.

Dama kuma kasar Saudi Arabiya da Dubai duk sun sanar da ganin watan Shawwal a kasashen su.

Share.

game da Author