Kwamitin dake binciken sama da fadi da akeyi da kudaden masarautar Kano ta bayyana cewa tabbas an gano wurare da dama da aka yi facaka da kudaden masarautar Kano karkashin Sarki Sanusi.
A bayanan da kwamitin ta mika wa sakataren gwamnantin jihar Kano, ta ce akwai wurare da dama da aka ga cewa an yi cuwa-cuwa da kudin masarautar.
Sannan kuma ta roki gwamnati da ta amince da shawarwarin da ta mika gabanta cewa wadda daya daga ciki shine ta dakatar da sarki Sanusi daga kujerar sa na sarkin Kano.
Kwamitin tace hakan zai bata daman yin aikinta da kyau ba tare da ana yi mata kulle-kulle ba daga fadar Sarkin.
Idan ba a manta Walin Kano ya bada bayanan yadda masarautar ta kashe kudadenta karkashin sarki Sanusi tun bayan nada sa sarki.
Ga bayanin a nan
Bisa zarge-zarge da wasu suke ta yi a kafafen sadarwa muka ga yakamata mu samar da ingantattun bayanai ga ‘yan jarida da kuma al’ummarmu ta kasar Kano.” In ji Walin Kano Alhaji Mahe Bashir Wali Mai rike da asusun kudin masarautar Kano.
Bamu gaji biliyan hudu daga asusun masarautar Kano ba, mun gaji biliyan daya da dubu dari takwas da casa’in da uku da dubu dari uku da saba’in da takwas da naira dari tara da ashirin da bakwai da kobo talatin da takwas (N1,893,378,927.38).
Domin kafin rasuwar marigayi Alhaji Ado Bayero Allah ya ji kansa, Muna da N2,875,163,431.17 amma a watan 7/2/2014 an biya (N981,784,503.79) na Ado Bayero Royal City. Shine ya zama an bar mana gadon (N1,893,378,927.38).
Don haka masu wancan batu na biliyan 6 basu yi lissafinsu dai-dai ba.
Daga cikin wadannan kudade mun cire sama da naira miliyan dari wajen biyan ‘ya’yan marigayi Sarki Alhaji Ado Bayero Allah ya ji kansa kudin motocinsu wadanda ake amfani dasu a gidan wanda suka ce ba na masarauta bane kyauta ce aka bawa mahaifinsu.
Masarautar ta samu amincewar sayo motoci masu silke (bullet proof) tun bayan harin ta’addanci da aka kaiwa marigayi mai martaba Sarki Ado Bayero a yayin dawowarsa daga wajen saukar Al’kur’ani a masallacin Murtala, kuma an saye su guda biyu N142,800,000.00 bisa doka ta takarda mai lamba SSGs Letter No SSG/S/D/A/26/T1/109 of 17th September 2014.
Su kuma motoci 2 samfurin Rolls roys masu lambar MS 1 da MS 2 kyauta ce wasu abokanan Sarkin suka bashi dan haka babu inda aka fitar da kudinsu daga asusun masarautar Kano.
Masarauta ta biya N152, 627,723.00 Dobo Gate don maida kayayyakin masarautar wadanda suka hada da kujeru da gadaje da fankoki domin bayan rasuwar Sarki marigayi Ado Bayero an kwashe duka wadannan kaya na amfanin gidan masarautar.
Sannan bayan hawan wannan Sarki yayi kokarin ciyar da hakimai da dagatai da duk ma’aikatan masarauta gaba daya tare da yi masu Karin albashi, don haka aka kafa kwamitin tsare-tsaren yin wannan aiki kuma masarauta ta amince da bayanansu. Inda aka daga darajar albashi daga N9.910 zuwa N36 Million a kowanne wata.
Anyi wannan kari bisa doka tare da amincewar gwamnati a takadda mai lamba KEC/CF/FIN/1/96 of 15th September 2014.
Maganar gyare-gyare na kwaskwarima da aka yiwa gidajen Sarki na Fadar Kano da Nasarawa da kuma Dorayi an yi wannan aiki ne bayan amincewar gwamnatin jiha da shedar takadda KEC/CF/FIN/VOL.1/T.11 of 17th oct.
Zancen shatar jirgin sama wanda shima aka yi zargin Sarki na dauka a aljihun masarauta sau biyu ne kacal ya dauki shatar jirgi, shima domin daukar hakimai da sauran ma’aikatan fada domin tafiya Sokoto wajen yin mubaya’a lokacin da aka nada shi Sarkin Kano wannan kuwa al’ada ce ta tanada, haka kuma an taba daukar shatar jirgi zuwa Nijar lokacin da marigayi Galadiman Kano ya wakilci masarautar Kano a wani taro a kasar Nijer.
Akwai wasu kudade miliyan 154 da aka yi zargin an fitar dasu ba bisa ka’ida ba, suma kuwa wadannan an fitar dasu ne domin biyan kudin motocin da aka kaiwa mai martaba marigayi Ado Bayero hari a yayin da yaje Masallacin Murtala saukar al’kur’ani Mai girma.
Ba’a biya cikakkun kudaden shiga bisa kaso 3% daga cikin 10% da masarauta take karba daga hannun gwamnatin jihar Kano wanda ake bata cikin arzikin kananan hukumomi 44 ba tun daga 2012, sai dai al’amuran sun dan gyaru daga 2016 amma an cike gurbin kudaden da gwamnatin bata biya ba na baya na 2014/2015.
Wannan ya sanya sai da aka rage wasu allowances na ma’aikatan wannan masarauta a shekarar 2016 inda ya zamto maimakon N36 Million ana biyan N27,467,206.01.
Sai kuma kudade da aka kashe wajen biyan kudin waya da Data wannan kam kudade ne da aka tattara na tsawon shekaru 3 ciki kuwa har da wayoyin da aka yi daga kasashen waje wato (roaming). Bisa al’adar Mai martaba kuwa daman waya daya ce tal da shi ta Airtel wacce yake amfani da ita gida da waje.
Sannan a shirye muke mu bayar da hadin kai koda ana neman wani karin bayani don bamu taba fitar da wasu kudi ba bisa ka’ida ba.
Mu kan yi budget ne duk shekara mu fitar da kudin da masarauta take bukata bisa yadda doka ta bamu ikon yi.
Ina rokon Allah don tsarkin sunayensa, ya kare Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da daukacin jama’ar jahar Kano da arewa da Najeriya baki daya, daga dukkan tashe-tashen hankula, ya zaunar da mu lafiya, amin.