Hukumar EFCC ta bayyana cewa Ofishin Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a na da karfin ikon da doka ta ba shi na karbe shari’a daga hannun EFCC ya maida ta a karkashin ofishin sa.
Kakakin Yada Labarai na EFCC, Tony Orilade ne ya bayyana haka a yau Lahadi a Abuja.
Orilade ya yi wannan raddi ne dangane da maganganun da ake ta yayatawa a kan yadda EFCC ta bayyana wa Babbar Kotun Tarayya sanarwar janye hannu daga shari’ar da ta gurfanar da Sanata Danjuma Goje.
EFCC ta maka Sanata Goje Kotu, shekaru takwas baya a na tafka shari’ar zargin sa da wawure naira biliyan 25 daga baitilmalin jihar Gombe a lokacin da ya yi gwamnan jihar tsawon shekaru takwas.
“Dalili kawai shi ne saboda Ofishin Antoni Janar na Tarayya ya karbe shari’ar daga ofishin mu, ya maida ta ofishin sa.
“Kuma dokar kasar nan ta bai wa wannan ofishi ikon karbe shari’a ko bincike daga ofishin EFCC zuwa ofishin ta.
“Wannan shi ne abin da ya faru.” Orilade ya karanto dokar Najeriya, Sashe na 174(1a) na Kundin Dokokin 1999, wanda ya bai wa ofishin Antoni Janar wannan karfin iko.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Hukumar EFCC ta sanar da tsame hannun ta daga shari’ar zargin wawurar kudade naira bilyan 25 da ta ke yi wa tsohon gwamnan Jihar Gombe, Danjuma Goje.
Ana tuhumar Goje da laifin wawuwar naira biliyan 25 ko kuma yin facaka da su, a lokacin da ya na gwamnan jihar Gombe, a tsawon shekaru takwas da ya yi ya na mulki.
Sai dai kuma Hukumar EFCC wadda ke zargin sa, kuma ita ce ta bincike shi tare da gurfanar da shi a kotu, ta sanar da janyewa daga shari’ar a jiya Juma’a.
EFCC ta yanke wannan shawarar janyewa daga shari’ar ce kwana daya rak bayan da Goje ya bayyana janye wa Sanata Ahmed Lawan takarar Shugabancin Majalisar Dattawa.
Goje ya bayyana wannan janyewa daga takara ne jim kadan bayan sun fito taro da Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ma ke goyon bayan Lawan din.
Abin da ya faru a jiya kotu, a jiya Alhamis shi ne: Yayin da aka kira shari’ar jiya Juma’a a cikin gaggawa, a gaban Mai Shari’a Babatunde Quadri, a Babbar Kotun Tarayya da ke Jos, sai lauyan EFCC, Wahab Shittu ya shaida wa kotu cewa hukumar EFCC ta janye hannun ta daga shari’ar, za ta damka shari’ar a ofishin Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a.
Lauyan EFCC wahab Shittu, ya ce daga can ne za a ci gaba da bin ba’asin gurfanar da Goje, ba daga ofishin EFCC ba.
“Ya Mai Shari’a, ai idan ma ka kula yanzu haka a cikin kotun nan, ga lauya nan daga ofishin Antony Janar da ya zo domin ya karbi shari’ar daga hannun EFCC, wato daga hannun mu.”
Lauyan Goje mai suna Paul Erokoro, ya shaida wa kotu cewa ba su da wata jayayya da janyewar da EFCC ta yi, ta damka gabatar da shari’ar a hannun ofishin Antoni Janar.
PREMIUM TIMES ta gano cewa, jim kadan bayan janyewar lauyan EFCC, sai lauyan ofishin Antoni Janar mai suna Pius Asika ya bayyana a gaban kotu, inda ya yi sanarwar karbar gabatar da karar.
Sai dai kuma ya roki kotu ta ba shi lokacin da zai yi nazarin tuhume-tuhumen da ake yi wa Goje, domin ya samu damar shiryawa sosai.
An daga karar zuwa 21 Ga Yuni, domin ci gaba da saurare.