Sojoji sun bindige masu sarrafa wa Boko Haram sakonni a yanar gizo ‘yan soshiyal midiya’ su tara

0

Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta sanar da bindige wasu ‘yan Boko Haram tara wadanda ta ce gwanayen sarrafa shafunan yanar gizo wato (soshiyar midiya) na Boko Haram.

Kakakin Sojojin Najeriya, Sagir Musa, ya bayyana cewa an kashe wadannan ‘yan soshiyal midiya su tara da sojoji su ka yi, ta kara tabbatar da cewa tuni an karya lagon Boko Haram, ta yadda ba su ma da wani habbasan kai hare-hare.

Ya bada sunayensu kamar haka: Abu Hurayra al-Barnawi, Ali al-Ghalam al-Kajiri, Abu Musab Muhammed Mustafa al-Maiduguri, Abu Abdullah Ali al-Barnawi, da Abu Musa al-Camerooni.

Ya bada sunayen wdanda aka bindige su tara cewa akwai: Abu Huraira Al-Barnawy, Ali al-Ghalam al-Kajiri, Abu Musab Muhammad Mustafa al-Maiduguri, Abu Abdullah Ali al-Barnawy da Abu al-Qa’qa al-Maiduguri.

Ya ce su na aiki ne wurjanjan a soshiyal midiya inda suke watsa farfahandar neman kafa Daular Musulunci.

An kama su ne makonni kadan bayan da mahukuntan sojoji da gwamnatin tarayya sun hakikice cewar an gama da Boko Haram.

Share.

game da Author