Dagaci ya maida fadarsa dakin karbar haihuwa da kula da marasa lafiya a Kaduna

0

Wani abin tausayi da yabawa ya auku a kauyen Kangimi-Ubangida dake karamar hukumar Igabi, Jihar Kaduna inda Dagacin wannan kauye ya maida fadar sa asibiti inda ake karbar haihuwa da dakula da marasa lafiya.

Dagacin mai suna Abdullahi Ubangida ya ce yayi haka ne ganin cewa mazauna wannan kauye sai sun yi tafiyar kilomita 20 kafin su isa asibitin Kawo wadda shine ya fi kusa da su. Duk da cewa wasu matan sukan garzaya asibitin dake Maraban Jos ne maimakon zuwa na Kawo.

” A dalilin rashin cibiyar kiwon lafiya a kusa da mu ya sa muna rasa mata da yara a kowani lokaci.

” Da na ga hakan ya na neman ya fi karfin mu, sai na garzaya cikin gari na tattauna da wasu malaman asibiti da Ungozoma da su rika zuwa kauyen mu suna duba marasa lafiya.

” A dalilin haka duk ranar Talata sai in shiga cikin gari in siyo magunguna kafin su malaman asibitin su zo. Sannan kuma dole na hakura na maida fada ta ta zamo asibiti karfi da yaji tunda bamu da asibiti a kauyen.

” Babban abinda muke bukata bayan asibiti shine dakin ajiye magani. Domin shima matsala ne babba da muke fama da shi.

Akalla jama’an kauyen Kangimi Ubangida sun kai mutane 40,000 kuma a cewar Abdullahi garin ta shekara 200 da aka kafata.

Maryam Musa dake da ‘ya’ya biyar ta ce mata sukan galabaita matuka wajen haihuwa a wannan kauye saboda rashin asibiti.

” Mata da yawa suna so su rika yin tsarin kayyade iyali amma saboda rashin sanin yadda za su yi da rashin wanda zai koya musu ya sa sun hakura sai haihuwa kawai suke yi. Sannan kuma da dama sun hakura da kokarin su nufi asibiti idan haihuwa ya zo sukan haihu ne a gida kawai duk saboda rashin cibiya ko asibiti da za su je.

Share.

game da Author