Shugaban Kamfanonin Dangote Group, Aliko Dangote, ya bayyana cewa matsawar Najeriya ba ta magance matsalar harken lantarki ba, watau makamashi, to a manta da duk wani tunani na ci gaban kasar nan.
Dangote ya yi wannan kakkausan gargadin ne a jiya Asabar, lokacin wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan batun hanyoyin inganta tattalin arzikin kasa da kuma dabarun ci gaban kasa a Lagos.
Ya kara da cewa hasken lantarki da makamashi shi ne hanya dorar a matakin farko na ci gaban kasa.
“Idan ba ku da ingancin hasken lantarki, to yaya za ku ci gaba. Ba ku da wuta, to ba ku da ci gaba. Wannan batu haka ya ke.” Inji Dangote.
Har ila yau, Dangote, wanda shi ne dan Afrika mafi kasaita wajen karfin arziki, kuma bakin da ya fi kowane bakar fata kudi a duniya, ya ce wata babbar matsalar kuma ita ce rashin tsara tafarkin da kasa za ta bi domin ta ci gaba.
“Kasar Masar duk da ba ta kai Najeriya a yawan al’umma ba, ta kara yawa da karfin haske da karfin makamashin ta zuwa migawatts 10,000 a cikin watanni 18.
“A Najeriya kuma yau shekaru 18 kenan mu na ta kiciniya da gaganiya ba tare da mun kara ko da migawatts 1,000 ba a cikin shekaru 18.
“Abin mamaki kuma Najeriya ta kashe kudade nunki uku fiye da abin da kasar Masar ta kashe? Me ya sa? Ya aka yi mu ka tsinci kan mu a wannan hali?
Daga nan kuma Dangote ya shawarci Najeriya ta inganta hanyoyin fitar da kayan sayarwar ta zuwa kasashen waje, tare da rage dogaro da shigo da kayan sayarwa daga kasashen waje.
Ya yi kira a kirkiro hanyoyin samar da kudaden shiga ingantattu a kasar nan, maimakon dogaro kacokan a kan danyen man fetur.
Dangote ya ce kamata ya yi ita ribar mai a rika tasarifin ta wajen gina manyan ayyuka a cikin kasar nan kawai. Ba wai a ce hatta biyan albashi, gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnatoci ma a ce sai an dogara da ribar danyen man fetur ba.
“Ban ga ta yadda za a yi harkokin kasuwanci su inganta ba, matsawar aka ce dan kasuwa babba da karami kowa shi ne zai samar wa kan sa lantarki ko makamashi.” Inji Dangote.
Ya shawarci gwamnati ta kara daukar harkar noma da muhimmanci. Sannan kuma ya yi kira ga Babban Bankin Tarayya (CBN) da sauran bankuwan kasuwanci su fantsama wajen bai wa kananan ’yan kasuwa basussuka domin inganta harkar kasuwanci da tattalin arziki a kasar nan.