Kungiyar Matasan Arewa ya bayyana cewa shi fa baya tare da zabin Tinubu da El-Rufai, wato Sanata Ahmad Lawan ya zama shugaban majalisar dattawa.
Shugaban kungiyar Shettima Yerima ya bayyana cewa tuni sun gano cewa zabin Ahmad Lawan ya zama shugaban majalisar siyasa ce kuma akwai wani boyayyar manufa da ke da nasaba da shirin tunkarar zaben 2023.
Kungiyar ta ce dole fa ‘yan Arewa fa su farga tun da wuri.
” Muna kira ga El-Rufai da Tinubu da su shiga taitayinsu su daina ya wa mutane wasa da kwakwalwa saboda siyasa domin mun gano kulke-kullen da suke shiryawa wadda ba zai haifar wa Arewa da mai ido ba a 2023.
” Idan baku manta ba dama can mun fadi cewa za a tilasta wa Danjuma Goje ya janye daga takarar shugabancin majalisar Dattawa din domin za a yi masa barazana da EFCC.
” Hakan kuma ya faru. An yi masa barazana da kayar EFCC da ta makale masa shekaru takwas kenan, cikin ruwan sanyi ya janye.
” Yanzu dai muna so mu sanar wa duniya cewa bamu tare da Ahmad Lawan, saboda kowa ya sani juyashi kawai za a rika yi.
Sai yadda wasu ke so ayi za a rika yi.
Kowa ya sani cewa idan dai maganar ‘Next Level’ ake yi tabbas Ali Ndume za abi a samu nasara. Shine zai yi tsayin daka wajen ganin an bi yadda doka take a koda yaushe.
Yanzu dai haka ya rage ga mai shifa rijiya, ko sanatoci su zabi wadda ya dace ko kuma su yi da na sani.