Kotun da ke sauraren karan zaben shugaban kasa ta yi watsi da karar da gamayyar jam’iyyu na C4C ta shigar gaban ta tana kalubalantar nasarar da Buhari yayi a zaben 2019.
Lauyoyin dake kare Buhari da jam’iyyar APC, Wale Olanipekun da Lateef Fagbemi sun bayyana wa kotu cewa basu ga takardar janye karar da C4C suka ce sun mika wa kotu ba sannan su kan su ba a mika musu ba.
A dalilin haka kuwa suna kira ga kotu da tayi watsi da wannan kara.
Saidai kuma kafin kotu ta jefar da wannan kara a kwandon shara, lauyan wadanda suka shigar da kara ya bayyana cewa a ranar litinin ne suka mika takardar janye karar sai da kuma ba su samu daman iya samu ya kaiga lauyoyin wadanda suke kara.
Alkalan wannan kotu su biyar cikin jagorancin Maishari’a mohammaed Garba yayi watsi da wannan kara.