Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, ta bayyana sanarwar kama wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban, har su 90 a cikin makon da ya gabata.
Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ahmed Iliyasu ne ya bayyana wa manema labarai haka a Hedikwatar Rundunar su da ke Bompai, Kano a jiya Juma’a.
Ya ce an kama wadanda ake zargin a farmakin da jami’an tsaro suka kai wurare da dama da aka yi zargin mabuyar batagari ce.
Iliyasu ya ce jami’an tsaro sun kai farmaki da samamen ne a ranakun Talata da kuma Laraba.
Daga cikin wurare da garuruwan da aka kai harin sun hada da Gano a cikin Karamar Hukumar Dawakin Kudu; Bachirawa a Karamar Hukumar Ungogo da kuma kan Titin Gidan Sarkin Kano, a cikin Karamar Hukumar Birni da Kewaye.
An kuma kama wasu a Dala, Panshekara, Kwana Hudu da kuma Dakata, duk a cikin Kano.
Daga cikin kayan lahanta jama’a da aka samu a jikin su, akwai wukake 64, almakashi da dama, gatari, awartakin datse karfe, layu da guraye, kullin tabar wiwi da kuma madarar sukudaye.
Ya kuma kara da cewa an kama wasu mutane biyu a Dala dauke da buhuna 14 na tabar wiwi, wadanda aka kiyasta jimillar kudin su zai kai naira milyan 5.
Ya ce an kuma kama wasu fitsararru 25 a kusa da Fadar Sarki, wadanda ake zargi da tayar da hankalin da ya yi sanadiyyar kisan mutum daya tare da ji wa wasu da dama raunuka.
An same su da wukake, addduna, sanduna, guraye da layu, gariyo da kuma kayan bugarwa.
Za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.