Kotu ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga Niels Hoegel, wani dan kasar Jamus da aka kama dumu-dumu da laifin kashe masara lafiya 85 a lokacin da ya ke aiki a matsayin ‘nas’ mai kula da marasa lafiya.
A ranar Alhamis ce aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai bayan da shi da kan sa ya amsa laifin rika yi wa marasa lafiya allurar kisa a wani asibitin kasar Jamus.
Asirin Hoegel dan shekara 42 ya fara tonuwa ne, bayan da aka same shi da laifin kashe wasu marasa lafiya biyu a cikin 2015.
An gano cewa Hoegel ya rika yi wa jama’a allurar dakatar da bugawar zuciya a asibitocin Oldenburg da Delmenhorst a kasar Jamus, daga 2000 zuwa 2005.
Daga nan kuma sai ya ci gaba da kashe marasa lafiyar babu kakkautawa.
Masu gabatar da kara sun ce Hoegel ya rika yin haka ne da nufin idan marar lafiya ya suma, sai ya farfado da shi domin wai ya burge likitoci ‘yan uwan sa tare da nuna musu kwarewar sa.
Da farko dai takardar zargin da aka yi masa ta nuna cewa ya kashe marasa lafiya 100.
Amma ya yi gardama, ya ce shi dai 43 kadai ya san ya kashe.
Dubun sa ta cika ne a lokacin da wani nas ya kama shi ya na danna wa wani majiyyaci allurar da ba ita likita ya rubuta cewa a yi masa ba.