Kotu ta bada umarnin a gaggauta bude AIT da Ray Power

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a gaggauta bude Gidan Talbijin na AIT da kuma Gidan Radiyon Ray Power da ke fadin kasar nan.

An rufe talbijin da radiyon mallakar kamfanin Daar Communcations a ranar Alhamis, bisa umarnin Hukumar Kula da Gidajen Radio da Talbijin ta Kasa, NBC.

NBC ta zarge su da karya dokar hukumar. Daga cikin zargin da ake wa AIT da Ray Power, har da watsa wasu bayanai da ka iya tunzura al’ummar kasar nan, wadanda aka watsa a soshiyal midiya.

Sai dai kuma wannan dakatarwa da aka yi wa AIT da Ray Power, ta janyo an rika sukar gwamnatin tarayya da NBC a kokarin su na murkushe ’yancin magana ko bayyana ra’ayi.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bayyana cewa tunda maganar ta na kotu tun ranar 30 Ga Mayu, to kamata ya yi kowa ya saurara ya ji hukuncin kotu tukunna.

A ranar 30 Ga Mayu ne dai Daar Communications a karkashin Shugaban Kamfani Raymomd Dokpesi, ya shigar da kara cewa kotu ta hana NBC katse mata shirye-shirye, ko toshe hanyar da masu kallo da sauraren radiyo ke ji da ganin su. Ko haka su watsa labarai ko bayanai, ko jawabai ko sharhi.

Ta kuma nemi kotu ta hana Gwamnatin Tarayya kulle harabar ofishin, ko hana ma’aikatan ta shiga ofisoshin su domin gabatar da shirye-shiryen su, har sai bayan da kotu ta ji ba’asin karar da Daar ya shigar a ranar 30 Ga Yuni tukunna.

Share.

game da Author