Rundunar ‘yan sanda ta sanar cewa ta yi nasarar ceto mutane 22 da wasu ‘yan kasar Chana biyar daga maboyar masu garkuwa da mutane a dajin Kaduna.
Sufeto-Janar Muhammed Adamu ya sanar da haka ranar Alhamis a takarda da ya raba wa manema labarai.
” A ranar 5 ga watan Mayu ‘Operation Puff Adder’ sun yi nasaran ceto ‘yan kasar Chana biyar a wasu dazukan Birnin Gwari.
An yi garkuwa da wadannan mutane ne ranar 15 ga watan Afrilu a Bobi jihar Neja.
Adamu yace a wannan maboyar masu garkuwa da mutanen ‘yan sanda sun kuma yi nasarar ceto mutane 22 da aka yi garkuwa da su tun daga jihar Zamfara.
Ya ce basu da tabbacin ranar da aka yi garkuwa da su da kuma adadin yawan kwanakin da suka yi a maboyar.
Adamu ya kuma kara da cewa ‘yan sanda sun yi arangama da masu garkuwa da mutanen inda suka yi nasaran kashe biyu daga cikin su.
Tun daga nada sabon Sufeto Janar din ‘Yan sandan Kasa Adamu, an kama ‘yan fashi da makami 275 da makamai 105.