Buhari ya sake ganawa da Shugabannin Bangarorin Tsaro

0

Shugaba Muhammadu Buhari na taron ganawar sirri da Shugabannin Bangarorin Tsaro, ciki har da Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu.

Kowane Shugaban Bangaren Tsaro da sauran hukumomin tsaro sun gabatar wa Buhari rahotannin da suke tafe da su.

Ya gana da su ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Aso Rock Villa yau Alhamis da rana.

Wadanda suka halarci taron na yau sun hada da Ministan Tsaro Mansur Dan Ali, Mashawarci a Fannin Tsaro, Babagana Monguno, Darakta-Janar na NIA, Ahmed Rufai, Darakta Janar na DSS, Yusuf Bichi.

Sauran sun hada da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Abba Kyari da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Najeriya na cikin halin mummunar matsalar rashin tsaro, musamman a Arewa, sakamakon hare-hare da yawaitar gaskuwa da mutane.

Dukkan wadanda Buhari ya yi wannan ganawa da su yau, su na shan suka saboda gaza dakile magalar tsaro da suka kasa yi.

Share.

game da Author