Kotu a magajin Garin Kaduna ta umurci Ester Morris mai shekaru 39 ta maida wa mijinta mai suna Tajudeen Musa sannan mai shekaru 46 Naira 500 kudin sadakin ta da ya biya a lokacin da za su yi aure.
Alkalin kotun Dahiru Lawal ya raba auren Ester da Tajudeen bayan tsawon shekara 11 suna tare sannan ya umurci wani ma’aikacin kotun da ya raka Ester gidan Tajudeen domin ya tabbatar Ester ta kwashe kayan ta kaf a gidan ta koma gidan su.
TSAKANIN ESTER DA TAJUDEEN
Dama can Ester da Tajudeen sun yi auren kotu ne shekaru 11 da suka gabata.
Ester dake zama a sabon barikin soja dake Afaka a Kaduna ta shigar da kara a wannan kotu domin ta raba auren ta da Tajudeen saboda rashin haihuwa da talauci da suke fama da su.
” Na auri Tajudeen shekaru 11 da suka wuce amma ban taba haihuba. Bayan haka kuma Tajudeen na zargi na da iyaye wai mun yi masa wata kulli ne da ya sa yake fama da bakin talauci.
Ester ta ce Tajudeen ya fara nuna mata alamun yana son su rabu bayan ya rika bayyana wasu halaye da bata san sa dashi ba.
Ta ce tana rokon kotun da ta raba auren ta da Tajudeen duk da cewa ya biya sadakin Naira 500 ne kacal a kanta.
Shi kuwa Tajudeen Titin Sardauna ya ce shima ya amince kotu ta raba auren sa da Ester.