‘Yan mata za su haifi jarirai miliya 70 nan da shekarar 2030 – UNICEF

0

Sakamakon binciken da asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) yayi ya nuna cewa ‘yan mata za su haifi jarirai miliyan 70 a duniya nan da shekarar 2030 idan ba a gaggauta daukan mataki ba.

UNICEF ta gudanar da wannan binciken a kasashe 176 tare da hadin gwiwar kungiya mai zaman kanta wato ‘Save The Children’.

Bangarorin da UNICEF da kungiyar suka duba yayin da suke gudanar da binciken sun hada da kiwon lafiya, ilimi, auren wuri, yunwa, kariya da sa yara aiki.

Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa nan da 2030 Najeriya za ta fi kasar India a yawan jariran da ‘yan mata za su haifa.

Sakamakon binciken ya nuna cewa kasashen yamma da tsakiyar Afrika sun sami nasaran rage kashi 19 bisa 100 na yawan yi wa yara kanana auren wuri sun kuma sami nasaran rage kashi 18 bisa 100 wajen dakile matsalar yunwa da yara ke fama da shi.

Kasashen da suka sani wannan ci gaba kuwa sun hada da Najeriya, Somalia,Sudan ta Kudu,Mali,Chadi,Niger da sauran su.

Share.

game da Author