Wani kungiya mai zaman kansa mai suna ‘Smart Mothers Foundation’ ya koka kan yadda ‘yan mata musamman a jihar Akwa-Ibom suka dulmiya sana’ar karuwanci saboda bakin talauci da yayi musu katutu da hatta audugan al’ada ke musu wahala.
Kungiyar ya bayyana cewa a dalilin haka za kaga ‘yan mata da dama na ta daukan ciki sannan ma su rasa yadda za su yi da shi a wasu lokuttan.
Jami’ar kungiyar sifon Udo ta koka da haka a taron inganta rayuwar yara da PREMIUM TIMES ta shirya a garin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom domin bukin ranar yara.
Udo ta bayyana cewa a yanzu haka kungiyar su na kula da ‘yan mata uku da suka yi ciki sannan basu da yadda za su yi.
Ta ce talauci, cudanya da baragurbin abokai, tarbiya duk daga cikin matsalolin dake haddasa haka.
Udo ta ce kungiyar su na horas da irin wadannan mata sana’o’in hannu domin su samu su iya tsayawa da kafafuwan su ba sai sun fada karuwanci ba.
Bayan haka Uduak Ekong shugaban kungiyar mata masu manema labarai reshen jihar (NAWOJ) da Imaobong Akpan sun koka da yadda mata ke ke shiga cikin kungiyoyin asiri da kuma rashin samun tarbiyya na gari.