Mataimakin shugaban jam’iyyar APC (Arewa) Lawali Shuaibu yayi kira ga shugaban jam’iyyarsa Adam Oshiomhole da ya gaggauta yin murabus.
A wasika ta musamman da ya rubuta ranar 27 ga watan Mayu, Lawali ya yi wa shugabancin Oshiomhole lakabi da ‘gurguntacciyar shuabanci’
Lawali ya koka cewa da gangar kuma da sanin shugaban jam’iyyar a rashin nasara da APC ta yi a kotu a jihar Zamfara.
“ Oshiomhole na da masaniya kuma dashi a ka shirya tuggun rasa kujerun da APC ta yi a jihar Zamfara. Sannan kuma jam’iyyar ta dauko hanyar tarwatsewa.
“ Ku duba ku gani, muna da jihohi 23 bayan zaben 2015 amma yanzu mun rasa 7. Muna da sanatoci 60 a 2015 yanzu muna da 57.
“ A kasashen da suka ci gaba, idan mutum ya gaza, tattara komatsansa yak e yi ya kara gaba.”
Kakakin jam;iyyar Lanre Issa Onilu ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta ce komai ba saboda wasikar ba ita aka yi wa ba.
Sai dai kuma Kakakin Oshiomhole , Simon Ebegbulem, bai masa kira da muka yi masa domin sanin ko wani mataki maigidan sa zai dauka game da wannan zargi.