Yadda za a ga sakamakon JAMB a saukake a wayar hannu

0

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Kasa (JAMB), ta bayyana cewa jarabawar JAMB ta fito yau Asabar.

Sannan kuma hukumar ta ce babu ruwan dalibi da zuwa cibiyoyin rubuta jarabawa domin ganin sakamakon da ya samu.

JAMB ta shawarci duk wanda ya rubuta jarabawar ta 2019, ya tura sako kalmar ‘RESULT’ ga wannan lamba 55019.

Amma zai yi amfani da lambar wayar da ya yi rajistar jarabawa da ita.

Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka a yau Asabar, a lokacin da ya ke sanarwar fitar da sakamakon jarabawar.

“Daga yau har zuwa ranar Litinin, wannan ce kadai hanyar da za a iya ganin sakamakon jarabawa.”

Ya ce sun fito da wannan tsarin ne domin hana ‘yan damfara su damfari mutane batun ganin sakamakon jarabawa.

Sannan kuma an fito da wannan dabara ce domin duk wanda bai ga sakamakon sa ba, to ya na daga cikin wanda aka rike sakamakon na sa kenan.

Sannan ya ce hakan ya na nufin an daina zuwa ana yin cunkoso a wurin duba jarabawa, inda wadanda ba su ga ta su ba ke yin dafifi a wuraren duba jarabawa ana haddasa cinkoso.

Oloyede y ace da ka tura sakon RESULT zuwa lambar 55019, to idan sakamakon ka ya fito, za ka ga an turo masa amsa cewa:

“Zuwa Gare ka, ga sakamakon zaben ka kamar haka….”

Idan kuma an rike maka sakamako ne, to za a turo maka sakon:

“RESULT WITHHELD”, wato “AN RIKE SAKAMAKON KA.”

Idan ka yi rajista amma ba ka rubuta jarabawa ba, za a turo maka sakon “CANDIDATE ABSENT”, wato “BA KA RUBUTA JARABAWA BA.”

Idan kuma an rike sakamakon ka, har zuwa lokacin da za a kammala wani bincike, to za a tura maka sakon: “AN RIKE SAKAMAKON KA sai an gama bincike a turo maka.”

Masu neman shiga jami’o’i su 1,826,839 ne suka rubuta jarabawar JAMB cikin wannan shekara, 2019.

An fito da sakamakon mutane 1,792,719 a yau Asabar.

Share.

game da Author