MAY 29: Bindow da makarraban sa na yin watandan kadarorin jihar Adamawa – Fintiri

0

A shirin rantsar da sabbin gwamnatoci da za ayi ranar 29 ga Mayu, zababben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya koka kan yadda gwamna mai barin gado Jibirilla Bindow da makarraba sa ke watanda da dukiyar jihar.

Kwamitin shirya mika mulki na bangaren zababben gwamna Fintiri ne suka koka da haka.

Shugaban kwamitin John Yahaya ya bayyana cewa a dan kwanakinnan kawai gwamnatin jihar ta rika bada kwangiloli masu yawa sannan ta na biyan su cif tun ba a yi su ba.

Bayan haka gwamnatin na raba wa makarrabanta wasu daga cikin kadarorin jihar ba tare da an bi doka ba.

” Sannan kuma tuni har gwamna Bindow ya biya kansa kudin sallama bayan ga dubban ma’aikatan jihar da bai-iya biyan su albashi ba duk da shiga watan Ramadana da aka yi.

” Kuma tun kafin a shirya yadda za a biya sabon tsarin albashi sai gashi har ya bayyana cewa jihar zata biya sannan kuma yana ta daukan sabbin ma’aikatan da bai dauka ba a da.

Sai dai kuma, kakakin gwamnatin jihar, Ahmed Sajoh, ya karyata wannan zargi cewa babu kamshin gaskiya a ciki.

” Kada kwadayin mulki ya rude su mana, har yanzu fa Bindow ne gwamnan jihar Adamawa, koko don zai tafi shi kenan sai a daina aiki a jihar?.

Sajoh ya karyata haka sannan ya ce gwamnati ba za ta yi abinda ba haka ba har zuwa ta fice daga gidan gwamnati ranar 29.

Share.

game da Author