Duk da umarnin da kotu ta bada cewa gwamnatin Kano ta dakatar da kirkiro sabbin masarautu a Kano, gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya nada sabbin sarakunan wadannan masarautu.
Ganduje ya ce ya riga ya nada sabbin sarakunan kafin hukuncin da kotu ta yanke na dakatar da shi.
Wadanda Ganduje ya nada kuwa sun hada
Ibrahim Abubakar II, Sarkin Karaye, Tafida Abubakar Il, sarkin Rano, Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi, Ibrahim Abdulkadir, Sarkin Gaya.
Idan ba Babbar Kotun Jihar Kano ta hana Gwamna Abdullahi Ganduje nada masarautu, har sai ta saurari karar da Gungun Mambobin Majalisar Dokokin Jihar ’yan jam’iyyar PDP suka kai gaban ta.
Jiya Juma’a ne mabobin jam’iyyar PDP a Majalisar Dokoki ta Jihar Kano suka garzaya kotu domin su hana Ganduje nadawa da kuma rantsar da sarakunan da ya nada a masarautu hudu da ya kara kafawa a lokacin da ya sa dokar daddatsa masarautar Kano.
Mambobin wadanda su ne marasa rinjaye, sun shigar da karar ca a bisa jagorancin Shugaban Masara Rinjaye, Rabiu Gwarzo, sun garzaya kotun domin neman a dakatar da Ganduje daga rantsar da nada sabbin sarakunan da ya yi niyyar yi a yau Juma’a, a bisa wasu dalilai biyar.
Sun bayyana wa kotu cewa ba a bi ka’idar da ya kamata a kira taron zama a zauren majalisa ba, kafin majalisa ta zartas da dokar karin masarautun guda hudu.
An yi zaman cikin gaggawa, kuma Gwamna Ganduje ya sa wa dokar hannu cikin gaggawa. Sannan kuma yay i gaggawar nada sakakunan, duk a cikin kwanaki biyu.
Sannan kuma a ranar ne Juma’a Ganduje ya shirya zai rantsar da su, kafin a shigar da karar taka masa burki.
Mai Shari’a Nasiru Saminu ya dakatar da Ganduje daga kirkiro Masrautun Gwarzo, Rano, Bichi da kuma Gaya.