Tsohon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja irin aikin da yay i da naira miliyan 400 da ya karba daga Gwamnatin Goodluck Jonathan.
EFCC ce ta gurfanar da Metuh a kotu, inda ta nemi a hukunta shi, domin ya san kudin ba ta hanyar da ta dace ya karbe su kuma aka ba shi su ba.
Cikin wata sanarwa da Kakakin EFCC, Tony Orilade ya fitar, ya ce Metuh ya yi wa kotu bayani dalla-dalla yadda ya kashe kudaden da ya karba.
EFCC ta ce Metuh ya ce ya kama hayar ofis ta hannun marigayi Tony Anenih, a kan kudi naira milyan 25.
Ya ce da sunan Anenih aka kama hayar ofishin, kuma sunan sa ne a kan cakin kudin da aka biya hayar.
“An zuba wa ofishin kaya na zamani kamar kwamfutoci, intanet, manyan janareto biyu, an dauki ma’aikata ana aiki ba dare ba rana.”
Metuh ya ce “an kashe naira milyan 37 wajen kafafen yada labarai da kuma ganawa da editocin jaridu a Najeriya.”
“An kashe naira milyan 13 da wasu milyan bakwai wajen daukar hayar kamfanonin jami’an tuntuba domin gudanar da ayyuka.”
“An kashe naira milyan 23 wajen gudanar da taron kara wa juna sani, ayyukan kamfen da kuma wasu miliyan 10 a kamfen a kafafen yada labarai na soshiyal midiya.
“An kashe naira miliyan 15 wajen buga kayan kamfen, jawabai a gidajen radiyo da sauran kafafen yada labarai.”
“An kashe naira miliyan 47 wajen samar da tsaro da kuma biyan alawus na kama wuraren taro da dakuna a otal-otal.”
“An kashe naira milyan 55 a Kudu-Maso Kudu, naira miliyan 97 a Arewa ta hannun marigayi Tony Anenih sai kuma naira milyan 1.4 da aka sayo lasifikoki da makirho-makirho
“ An kashe naira miliyan 40.4 a Kudu Maso Gabas, yayin da aka baiwa dukkan ma’aikatan da suka yi hidima naira 200,000 kowanen su. Ma’aikatan su 57 ne.”
Dalilin da yasa na ki yi wa kotu wannan bayanin a baya
Olisa Metuh ya shaida wa kotu cewa ya ki yi mata wannan bayani ne tun farkon fara shari’a a shekarun baya, saboda kawai yadda EFCC ke ta zugugutawa a cikin kafafen yada labarai ya danne naira miliyan 400.
Metuh ya nuna cewa idan ya yi wannan bayani, to shikenan to za a ci gaba da yanke masa hukunci a kafafen yada labarai, alhali kuma ita EFCC zargin sa ta ke yi.
Sannan kuma ya shaida wa kotu cewa irin yadda EFCC ta rika nuna ya ci naira miliyan 400, ya janyo an rika yi masa rubutu na batunci a jaridu ana nuna shi a matsayin wanda ya yi wa naira miliyan 400 na kudin sayen makamai hadiyar-kafino.
Metuh ya musanta cewa wai ya bai wa wani dan canji mai suna kabiru Ibrahim dala miliyan daya domin ya canja ko kuma a matsayin jari da ya zuba a kamfanin canjin sa ba.
Ya ce wannan duk ba gaskiya EFCC ta gabatar ba.
Za a ci gaba da shari’a cikin wata Yuni.