Buhari da Osinbajo sun bayyana kadarorin su

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bi dokar kasa ya bayyana kadarorin sa, inda ya damka wa Hukumar CCB fam din da ta ba shi ya cike.

Dokar Najeriya ta jaddada cewa tilas shugaban kasa da mataimakin sa sai sun bayyana kadarorin su kafin a rantsar da su.

A yau Laraba dai ne ake sake rantsar da Buhari a karo na biyu. Ya yi nasara a zaben 2015, kuma ya sake yin nasara a zaben 2019.

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa an dan samu canji a yawan kadarorin da shugaba Buhari ya bayyana ya mallaka a 2015, amma ba wani mai yawa ba.

Cikin bayanin da Kakakin Buhari, Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya cika fam din kuma tuni tun ranar Talata aka maida wa Shugaban Hukumar CCB, Mohammed Isa.

Shehu ya ce Babban Hadimin Shugaban Kasa a Harkokin Cikin Gida, Sarki Abba ne ya maida wa CCB fam din, a madadin Shugaba Buhari.

“Babu karin yawan gidaje, babu karin yawan asusun ajiyar kudade a cikin gida ko a waje, haka kuma babu karin hannayen jari.” Inji Shehu.

Ya kara da cewa Shugaban CCB ya jinjina wa Buhari da ya bayyana kadarorin sa kamar yadda doka ta tanadar.

Sai dai kuma har yanzu ba a iya tantance yawan wadannan kadarorin ba.

Duk da cewa Buhari ya yi alkawarin zai bayyana kadarorin sa idan ya ci zabe a 2015, bayan ya yi nasara bai yi haka din ba, har sai bayan da ya sha matsin lamba tukunna.

Ko a lokacin bayanai ne kawai aka, yi domin ba a bayyana wuraren da ya ce gidajen sa suke ba.

KADARORIN OSINBAJO

Kakakin Mataimakin Shugaban Kasa, Laolu Akande, ya ce Mataimakain Shugaban Kasa ya bi dokar kasa wadda ta ce ya bayyana wa CCB kadarorin sa kafin ranar rantsar dashi.

Akande ya ce Osinbajo ya mika bayanan na sa kadarorin jim kadan bayan da shugaban kasa ya mika na sa.

Babbar Jami’a Mai Bada Shawara a kan harkokin Shari’a Ga Mataimakin Shugaban Kasa, Bilkisu Saidu ce ta mika wa Shugaban CCB, Mohammed Isa bayanan kadarorin Osinbajo.

Akande ya ce babu wani canji da aka samu daga bayanan yawan kadarorin Osinbajo da ya bayyana a cikin 2015.

“Babu karin yawan gidaje, babu karin yawan tarin dukiya, babu karin yawan hannayen jari, kuma babu karin asusun ajiyar kudade.”

Share.

game da Author