Yadda hadama ya handame Yari, Yerima da APC a Zamfara

0

Masu yin sharhin siyasa da fashin baki sun yi ta tofa albarkacin bakunan su bisa ga hukuncin da kotu ta yanke da dakatar da APC da ‘yan takaran ta kaf da suka ci zabe daga darewa kujerar mulki sai bayan shekara hudu masu zuwa.

Wannan azal da ya fado wa jam’iyyar APC da ‘yan takaran ta a jihar Zamfara nuni ne cewa baka yin zamanin ka ka yi na wani.

Giyar Mulki

Tun farko dai mutum daya ne ya kira wa jam’iyyar da jihar ruwa. Wannan kuwa ba kowa bane illa gwamnan jihar mai barin gado wato AbdulAziz Yari.

Gwamnan jihar yayi kaurin suna matuka da yin bakin jini a jihar musamman idan aka rika tuna irin yadda mutanen sa ke ta fama da hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

An rika cewa gwamna Yari bai taka rawar gani ba wajen kawo karshen hare-haren mahara a jihar. Sai dai ya tare a Abuja kawai bai damu da abin da mutanen jihar ke ciki ba.

Yari ya rika taka duk wanda yaga dama da ya kai ga hatta gogan siyasar Zamfara wato Sanata Ahmed Sani Yarima ya kasa cewa uffan balle ko ya iya kwaban sa. Zura masa ido yayi giyan mulki na dibar sa.

Zaben 2019

A lokacin da zaben 2019 ya karato sai mutane da dama suka fito don fafatawa wajen neman kujerun siyasa na jihar, sai dai kash, gwamna Yari yayi babakere ya hana kowa sakat. Idan ba kai bane zabin sa wahalar banza kake yi kawai.

Daya daga cikin jiga-jigan da suka fito takaran sun hada da fitaccen dan siyasan nan, wato sanata Kabiru Marafa.

Kabiru Marafa ya fito don takarar gwamnan jihar, amma gwamna Yari yace bai isa ba, dole sai zabin sa wato kwamishinan kudin jihar, Mukhtar Koguna.

Yayi babakere ya hana a gudanar da zaben fidda gwani a jam’iyyar APC din. Aka yi juyin duniya ya bari ayi zaben fidda gwanin yaki yarda ayi.

Haka fa aka yi ta kai ruwa rana tsakanin sa da ‘ya’yan jam’iyyar da suke wasa takubban su cewa ba gudu ba ja da baya, sunanan kan bakan su cewa lallai sai anyi zaben fidda gwani kuma ba za su yi zabin Yari ba wato Mukhtar.

Bayan kwanaki sai Yari ya ce wai anyi zaben fidda gwani amma irin wanda ake amincewa bai daya, wato na kowa ya bi.

Hakan bai yi musu dadi ba bayan mika wa uwar jam’iyyar sunayen da zabin sa ne ba na ‘ya’yan jam’iyyar ba.

Sanata Kabiru Marafa tuni ya garzaya kotu inda ya rika kalubalantar wannan matsayi na gwamna Yari.

Marafa ya shaida wa kotu cewa lallai jam’iyyar APC ba ta yi zaben fidda gwani ba a jihar Zamfara.

Kotun daukaka kara ce ta fara yanke hukuncin cewa lallai jam’iyyar APC ba ta yi zaben fidda gwani ba. Daga nan sai APC da da Yari suka lula sai kotun Koli.

Anan ma ba suyi nasara ba.

Yanzu dai jam’iyyar APC da ‘yan takaran ta duk sun zama ‘yan kallo har sai 2023, wani abu wai batan bakatantan.

Share.

game da Author