Hukumar Tsaro ta Sojojin Sama ta bada sanarwar yin ruwan wuta da wasu sojojin ta suka yi wa maharan Boko Haram.
Sojojin saman dai na ‘Operation Lafiya Dole’, sun yi wa Boko Haram ruwan wuta ne a wajen Tumbun Hamma da ke jefen Tafkin Chadi a Barno.
Kakakin Hukumar Tsaro ta Sojojin Sama, Ibekunle Daramola ne ya bayyana haka a Abuja, tare da cewa a ranar Juma’a ne aka kai musu harin wanda aka yi wa Boko Haram din babbar barna.
“An kai musu farmakin ne da jiragen yaki, bayan da aka samu rahon sirri cewa, Boko Haram din da Sojojin Najeriya, Nijar da Chadi suka kai wa farmaki ta sama a Malkanori da Tungar Rego, sun yi dandazo a Tumbun Hamma.” Inji Ibekunle.
Ya kara da cewa bayan an yi nazarin daidai inda suke da kuma nazarinn daidai wurin, an yi amfani da jirgin yaki samfurin Alpha Jet, aka kai musu farmaki ta sama.
Ya ce annkashe da dama daga Boko Haram, aka lalata musu kayayyaki, mabuya da makamai.
Daramola ya kara da cewa sojojin sama za su ci gaba da kai farmaki tare da na kasa, har sai sun kakkabe Boko Haram.