YOYON FITSARI: An yi wa mata 43 Fida a asibitin JUTH

0

Wasu kwararrun likitoci sun yi wa mata 43 dake fama da matsar yoyon fitsari fida a asibitin koyarwa na jami’ar Jos, Jihar Filato.

A cikin matan da aka yi wa aikin akwai wata tsohuwa mai shekaru 82 da wata yarinya ‘yar shekara tara kuma anyi wannan aiki ne duk a kyauta.

Shugaban asibitin JUTH kuma jagoran likitocin Edmund Banwat ya bayyana haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranan Lahadi a garin Jos.

Ya ce likitocin sun yi haka ne tare da hadin gwiwar kungiya “Safe Motherhood Partners’’ domin wayar wa mutane kai kan cutar sannan da tallafa wa matan dake fama da cutar.

” A lissafe kudin yin fidar yoyon fitsari ya kan kai Naira 200,000 kuma mafi yawan matan dake fama da wannan matsala basu da karfin biya wa kansu kudin aikin.

Banwat ya ce mafi yawan matan da suka yi wa fida sun kamu da cutar ne a dalilin doguwar nakuda amma na ‘yar shekara tara ta kamu da cutar ne a dalilin wasu miyagun al’adun gargajiya kamar yi wa mace kaciya.

” Kamar yadda aka sani mace kan kamu da yoyon fitsari ne a dalilin doguwar nakuda ko kuma idan shekarun ta na haihuwa basu kai ta fara haihuwa ba.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya koka kan illar da yoyon fitsari ke yi wa mata inda ya bayyana cewa rashin daukan mataki don ceto rayukan mata ka iya yin ajalinsu.

Adewole ya ce bincike ya nuna a duk shekara akan samu matan dake fama da wannan matsala da suka kai 12,000 zuwa 15,000.

Ya ce yawan ya karu zuwa 20,000 sannan a Najeriya akwai mata 400,000 zuwa 800,000 dake fama da wannan matsala.

Adewole ya ce koda yake ana iya warkewa daga cutar ta hanyar yin aiki, amma kamata ya yi a rika bari yara na yin kwari kafin ayi musu aure sannan a rika ganin likita a duk lokacin da ake dauke da ciki.

Share.

game da Author