An kama wata dake shigowa fursinoni muggan kwayoyi a gidan yarin Kano

0

Jami’an Hukumar Kula da gidajen Yari ta kasa reshen jihar Kano sun kama wata mata mai suna Rifkatu Anthony dake shigowa gidan tana rabawa fursinoni muggan kwayoyi.

Jami’an hukumar ya ce an kama Rifkatu ne a daidai tana kokarin shiga gidan da wani kwali.

Da aka matsa da bincike sai aka gano cewa ashe kulli tabar wiwi ne har guda 39 a ciki zata shiga wa fursinonin da shi.

Ita dai Rifkatu ta ce sako ne zata kai ma wani a cikin gidan yarin. Tace wani mai suna ThankGod ne ya bata wannan kwali.

Shugaban hukumar reshen jihar Kano Gambo Abdullahi ya yabawa jami’an da suka kama wannan mata sannan ya kara da cewa hukumar ba za ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta rika kama irin wadannan mutane da ke shigo wa fursinoni kwayoyi cikin gidan yari.

Share.

game da Author