Wasu da ake zargin Boko Haram ne sun kai wani samamen farmaki a wani sansanin sojoji, suka kashe 15, tare da ji wa wasu 19 raunuka.
Majiyar cikin sojoji ta tabbatar da kai wannan farmaki a kan sojojin Najeriya, tare da cewa ranar Juma’a ne aka kai harin.
’Yan ta’addan sun yi wa Karamar Hukumar Magumeri shigar-kutse, suka yi kaca-kaca da wani sansanin soja wajen karfe 6 na yammacin ranar Juma’a. Haka PREMIUM TIMES ta samu cikakken bayani.
Majiya ta ce cikin sojojin da suka rasa rayukan su, har da wani kaftin da laftanar da sauran masu kananan igwai su 13.
PREMIUM TIMES ta boye sunayen sojojin da suka rasa rayukan su, domin ta bai wa hukumar sojoji damar sanar wa iyalan su da kan ta.
An kuma tabbatar da ji wa wasu sojojin su 19 raunuka, wadanda tuni aka kwashe su zuwa wani asibitin sojoji a Maiduguri domin kula da su.
Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa, wato AFP, ya ruwaito wannan labari tun jiya Juma’a cewa sauran sojoji 24 da ke sansanin sun fice zuwa wani wuri na sojoji da ya fi inda suke kwakkwaran matakan tsaro.
Sai dai kuma ba a kai ga sanin adadin Boko Haram ko nawa ne suka rasa rayukan su ko aka ji wa raunuka ba.
Amma dai Boko Haram bangaren ISWA sun yi ikirarin su ne suka kai harin.
An kuma ruwaito cewa maharan sun sace manyan makamai, har da mashing ta harbor jiragen yaki da motoci kirar Toyota Hilux, duk suka arce da su.
Sannan kuma har yanzu sojoji ba su fitar da wani jawabi dangane da harin ba. kuma an kira wayar kakakin su amma bai dauka ba, a jiya Juma’a da dare.