RAMADAN: Kayan abinci ya yi tashin gwauron Zabi a kasuwanni

0

Musulmai a fadin duniya na shirin fara azumin watan Ramadan ranar Litini ko Talata.

Hakan ya sa ma su siyarda kayan masarufi sun fara tsawwala ya mutane tsada.

A jihar Legas, abin bai canja zani ba domin kuwa kayan abinci sun fara tsada matuka.

Da wakilin kamfanin dillancin labaran Najeriya ya garzaya wasu kasuwanni a Legas ya gano cewa kayan abinci musamman kayan miya sun yi tashin gwauron zabi saboda tunkarowar azumi.

Kwandun tumatir da ake siyarwa naira 5000 a makon da ya gabata ya ninka zuwa naira 12,000.

Haka wasu kayan abincin kamar su Atarugu da albasa.

Mutane sun fara kokawa kan yadda ‘yan kasuwa suka maida watan Ramadan lokacin tsawwala wa mutani tsada.

Wani dankasuwa ya cewa akwai yiwuwar samun sauki idan aka fara shigo da kayan miya zuwa kasuwannin jihar har daga kasar Kamaru.

Share.

game da Author