Hukumar Tsaron Sojojin Najeriya ta bayyana cewa akwai marasa kishin Najeriya da ke kulle-kullen tuggu tare da wasu ’yan kasashen waje, domin su kawo cikas ga bikin sake rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 Ga Mayu.
Sanarwar ta ce su na kokarin yin haka ne domin su gurgunta tafarkin dimokradiyya a Najeriya.
Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Sagir Musa ne ya bayyana wannan kakkausan bayani a cikin wata takardar ya fitar ga manema labarai, jiya Asabar.
Musa ya ci gaba da cewa, “wasu marasa kishin kasar nan na shirin su kawo rudani ta hanyar tuggu da kuma kirkiro matsalar tsaro, musamman a cikinnkasar nan kuma wannan bangaren yanki na Afrika ta Yamma.”
Ya kuma kara da cewa wadannan tsiraru na ci gaba da kokarin ganin sun ingiza Boko Haram da mahara sun dumbuza musu kudade da saura kayan da suke bukatu.
“Irin munanan kalaman da ke fitowa daga bakunan su, ya nuna sun a bada goyon baya ne a fakaice ga mabarnata.
“Misali, wata kwakkwarar majiya ta nuna cewa wasu tsiraru na kulla mummunar alaka da Boko Haram, yayin da wasu kuma kiri-kiri su na kirkirar karairayi ga jami’an tsaro, da nufin haifar da fudani tsakanin sojoji da fararen hula da kuma gwamnati.
“Sannan kuma sun a kashe guiwar jami’an tsaro ta hanyar kirkirar labaran karairayi.” Inji Sagir Musa.
Daga nan sai ya ja kunnen su kuma yay i tsokaci a kan cewa idan ba a daina ba, to abin ba zai yi wa duk wani mai yin haka din dadi ba.
“Akwai kuma wasu daga kasashen waje da ke aiki ba ji ba gani domin haifar da rashin jituwa a tsakanin sojojin Gayammyar Kasa-da-kasa, wato MNJTF, da nufin samar da kafar yadda ISWAP da kuma reshen sun a Boko Haram su sake samun girndin zama.
Yayin da ya ce sojoji ba za mu mika kai borin wasu tsirarun batagari ya hau kan su ba, ya kuma ce sojojin Najeriya su na goyon bayan kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen ganin an dakile ta’addanci gaba daya a kasar nan.
A karshe ya ce sojojin Najeriya a ko da yaushe su na masu biyayya ga mulkin dimokradiyya da kuma Gwamnatin Najeriya.
Sun kuma maida hankali domin ganin sun kakkabe ’yan ta’adda da magoya bayan su gaba daya.