Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) ta kama wasu jami’an ma’aikatar wasanni da matasa a Abuja da laifin yi wa ‘yar shekara 13 fyade.
NAPTIP ta sanar da haka a wani takarda da ta aika wa PREMIUM TIMES ranan Alhamis.
A takardar NAPTIP ta bayanana cewa Salisu Sabiu mai shekaru 55 da Ibrahim Mansur mai shekaru 51 sun aikata wannan ta’asa ne a unguwan Dutse dake Abuja.
Sabiu da Mansur sun yi wa ‘yar makwabcin su mai shekaru 13 fyade. Wani mazaunin unguwar ne ya tona musu asiri inda ya sanar wa hukumar NAPTIP din.
A yanzu haka Sabiu da Mansur sun amsa laifin su sannan za a hukunta su bisa ga tsarin doka.
A karshe shugaban NAPTIP Julie Okah-Donli ta yi tir da haka sannan ta bayyana cewa hukumar ba za ta yi kasa kasa ba wajen ganin ta hukunta duk masu aikata munanan aiyukka irin haka.
Juli ta kuma yi wa mutane tunin cewa hukumar na nan a kan bakanta na biya da kare rayukan mutanen da suka tona asirin masu aikata miyagun aiyukka irin haka.