PDP ta ce tilas mambobin ta su shiga takarar zaben Shugabannin Majalisa

0

Jam’iyyar PDP ta sake jaddada matsayin ta cewa don mambobin ta ba su da rinjaye, ba za a iya hana su shiga takarar mukaman da su ke so a majalisa ba.

PDP, wadda ita ce jam’iyyar adawa a yanzu ita ce babbar jam’iyyar adawa, ta ce har yanzu ba ta tantance wanda za ta goya wa baya ba a Shugabancin Majalisar Tarayya da ta Dattawa.

A zaben 2019, APC ce ke da rinjaye a Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa. APC na da sanata 60 daga cikin 109, sannan ta na da Mamba 220 daga cikin 360.

Duk da ana sa ran APC ce za ta fitar da Shugabannin Majalisu, alamomin rashin jituwa da kuma hadama na iya sa PDP ta tsinci dami-a-kala.
Ko kuma duk wanda zai zama shugaban majalisa, dole sai ya nemi hadin kan mambobi da sanatocin PDP.

APC dai ta jajirce tilas sai ta samar da Shugaba da Mataimakin sa a Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa.

Ita dai APC ta fitar da cewa a zabi Sanata Ahmed Lawan da Hon. Femi Gbajabiamila.

Sai dai kuma akwai wadanda suka jajirce cewa sai an yi zabe, duk mai sha’awa ya fito takara.

Kakakin Yada Labarai na PDP Kola Olabondiyan, ya ce har yau PDP ba ta jaddada goyon bayan ta a kan kowa ba tukunna.

Share.

game da Author