Gwamnati ta ware Naira biliyan 9.2 domin gina makarantu da siyo maganin cutar Kanjamau

0

Gwamnatin tarayya ta amince ta ware Naira biliyan 9.2 domin gina makarantu irin na zamani guda bakwai da siyo maganin cutar Kanjamau a Najeriya.

Ministan yada labarai Lai Muhammed ya bayyana haka ranar Alhamis bayan an tashi taron kwamitin zartaswa da aka yi a fadan shugaban kasa a Abuja.

Mohammed ya ce gwamnati za ta yi amfani da Naira biliyan 4.6 daga cikin wadannan kudade wajen gina makarantun zamani a jihohin Legas, Katsina, Nasarawa, Bauchi, Edo,Imo da babban birnin tarayya Abuja.

A karshe yace gwamnati za ta kasa sauran kudin da ya rage wajen bada kwangilan siyo magungunan cutar kanjamau domin masu dauke da cutar a kasar nan.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA) ta bayyana cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar kanjamau a Najeriya.

Shugaban hukumar Sani Aliyu ya bayyana haka cewa bisa ga sakamakon binciken da hukumar ta gudanar a shekarar 2018.

Daga watan Yuli zuwa Disambar 2018 hukumar NACA ta fara gudanar da wannan binciken domin gano adadin yawan mutanen dake dauke da cututtukan kanjamau, Hepatitis B da C domin gwamnati ta tsara hanyoyin inganta kula a kasan.

Sakamakon binciken ya nuna cewa mutanen dake dauke da cutar kuma masu shekaru 15 zuwa 49 sun kai kashi 1.4 inda daga ciki kashi 1.9 mata ne sannan kashi 0.9 maza.

Sannan adadin yawan mutanen dake dauke da cutar kuma ke samun kula dake da shekaru 15 zuwa 49 sun kashi 42.3 inda daga ciki kashi 45.3 mata ne sannan kashi 34.5 maza.

Binciken ya kuma kara nuna cewa yankin kudu maso kudu ce ta fi samu yawan mutanen dake dauke da cutar a kasar nan inda yawan su sun ya kai kashi 3.1.

A Arewa ta tsakiya mutanen dake dauke da cutar sun kai 0.2, kudu maso gabas kashi 1.9, kudu maso yama kashi 1.1, arewa maso gabas kashi 1.1 sannan arewa maso yamma kashi 0.6.

Share.

game da Author