Gungun wasu masu masu zanga-zanga a karkashin kungiyar Kano First Forum, ta yi Allah-wadai da sa hannun da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje yayi wa dokar da ta dattatsa masarautar Kano zuwa gida biyar.
An gudanar zanga-zangar a karkashin jagorancin Yusuf Rabiu jiya Alhamis, ganin yadda mambobin majalisar suka yi gaggawar zaman amincewa da dokar da ta daddatsa masarautun da kuma yadda a lokaci guda Ganduje ya sa mata hannu nan take.
Sun rika daga kwalayen da suka yi wa rubuce-rubuce iri daban-daban: “Ba karin masarautu ne ya dame mu ba”. “Ilmi, ruwa, tsaro da zaman lafiya ne ya fi damuwar mu. “Ba mu son dokar da ba ta kan turbar dimokradiyya. Ba mu amince a siyasantar da sarautar sarkin Kano ba.”
Sun yi zuga har a kan hanyar Gidan Murtala, inda daga baya ’yan sanda suka tarwatsa su.
Yayin da shugaban zanga-zangar ke wa manema labarai jawabi, Rabiu y ace ya kamata Ganduje ya fahimci bambancin da ke tsakanin Sarki da kuma Masarautar Kano.
Ya ce don kawai gwamna na so ya dauki wani mataki a kan Sarkin Kano, bai kamata fushi ya kwashi zuciyar sa har ya yi wa masarautar Kano illa ba.
Rabiu ya kara da cewa banda rabuwar kawuna babu abin da karin masarautu zai janyo a Kano.
“Wannan kirkiro masarautu biyar zai rarraba kawuna a Kano. Ga tulin matsaloli nan da ke addabar Kano wadanda su ya kamata ’yan majalisa su maida hankali a kan, matsalar ilmi, ruwa, kiwon lafiya durkushewar kasuwanci a Kano.
“Amma duk gwamna da ‘yan majalisa bas u dubi wadannan ba, duk da matsalar marasa aiki milyan 3.5 da muke da su a Kano, sai suka dauki turbar ruguza kyawawan tarihin masarautar Kano mai muhimmancin da ta wuce shekara 1000 da kafuwa.” Inji Rabiu.