Dalilin da ya sa na daddatsa masarautar Kano – Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ya kirkiro masarautu hudu a jihar Kano ne domin ci gaban jihar.

Idan ba a manta ba Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu guda hudu a jihar Kano bayan wata kudiri da majalisar jihar ta mika wa gwamnan bayan amincewa da a sake fasalin masarautun jihar.

Tuni dai har gwamna Ganduje ya rattaba hannu a akai ta zama doka.

Dokar ya kirkiro sabbin manyan masarautu har guda hudu da suka hada da masarautar Karaye dake da kananan hukumomi 8 a karkashinta, Masarautar Bichi dake da kananan hukumomi 9, Masarautar Rano dake da kananan hukumomi 10 sai kuma masarautar Gaya dake da kananan hukumomi 9 dakuma masarautar kano dake da kananan hukumomi 8 ita ma.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne zai zama shugaban majalisar sarakunan Kano din, sai dai kuma za ta riga zazzagayawa ne.

Mutane da dama da suka tofa albarkacin bakin su game da abin da gwamnan ya yi sun ce Ganduje yayi haka ne domin ci wa sarkin mutunci saboda kin yin sa da abi yi ba.

” Duk irin wadannan mutane da ke fadin haka sun suna da hurumin fadin abinda suke so. Mu dai mun yi haka ne domin ci gaban jihar.

” Ba na yi wa sarkin Kano Sanusi bita da kulli. Ya kamata ace shine ma yake tuntuba na game da irin haka domin ci gaban jihar.

Ya ce mutanen jihar Kano na murna da Kirkiro wadannan masarautu da gwamnati ta yi sannan ‘‘ Za mu yi kokarin ganin masarautun sun samar da ci gaban da ake bukata a jihar.”

Share.

game da Author