Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta gargadi ’yan jarida su daina azarbabin yin sharhi

0

Shugabar Kotun Daukaka Kararrakin Zaben Shugaban Kasa, Zainab Bulkachuwa ta yi barazanar cewa za ta yi maganin lauyoyi, masu kai korafe-korafe da ’yan jarida da aka kama sun a yin sharhin duk wata karar da ke a gaban kotun.

Bulkachuwa ta ce duk lauyan da aka kama ya na sharhin kararrakin a kafafen yada labarai bayan zaman kotu, to Kotun Daukaka Kara za ta yi maganin sa.

Ta yi wannan gargadin a wurin da ta ke kaddamar da fara zaman kotun a ranar Labarar da ta gabata a Abuja.

Ta ce irin wadannan rubuce-rubucen da sharhin na kawo wa kotu cikas da kuma tarnaki ga yanke hukunci. Kuma ya na jefa waswasi ga jama’a a kan hukuncin da kotu za ta yanke.

“Mun sha ganin yadda wasu ke rika yin rubuce-rubuce a soshiyal midiya ko surutai a gidajen radiyo da talbijin su na yanke hukunci mai laifi da mai gaskiya a a wasu shari’o’in da ke gaban kotu da ba a rigaya aka yanke musu hukunci ba.

“Mu na fata da kuma addu’a cewa a wannan karo ba za mu ci karo da wadannan matsalolin ba, domin alfanun wannan kasa. Ba mu tsammanin jin wasu lauyoyi su rika fita sun a surutai barkatai ko rubuce-rubucen da zai kara zafafa shari’un da ke a gaban kotu.” Inji Bulkachuwa.

A karshe ta ce wannan gargadi bai tsallake kan jam’iyyun siyasa da magoya bayan su ba.

Share.

game da Author