Kungiyar likitocin kasar nan (NMA)na yankin kudu maso kudu reshen jihar Ribas ta sanar cewa masu garkuwa sun sako Ogbonna Uchenna -Aju ranar 9 ga watan Mayu.
Kungiyar ta sanar da haka a wani takarda da ta raba wa manema labarai ranar Lahadi.
A takardan kungiyar ta bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun sace Ogbonna a hanyar sa ta dawowa gida dake karamar hukumar Obudu daga ga karamar hukumar Ogoja duk a jihar Ribas.
A dalilin sako Ogbonna da masu garkuwan suka yi kungiyar NMA ta dakatar da yajin aikin da ta fara.
Dama can kungiyar NMA ta fara yajin aiki a dalilin sace wannan likita da aka yi inda ta ce ba za ta dawo aiki ba har sai an sako likitan.
” Daga yanzu kungiyar NMA shiyar Kudu maso Kudu na kasar nan za ta shiga yajin aiki a duk lokacin da aka yi garkuwa da ma’aikatan kiwon lafiya.
Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su kara zage damtse wajen samar wa mutanen Najeriya tsaro.