Shayar da jarirai nonon uwa zai taimaka wajen rage mace-macen su da ake fama dashi – Kwararru

0

Jami’ar kungiya mai zaman kanta ‘Alive & Thrive’ Toyin Adewole-Gabriel ta yi kira ga mata kan shayar da jariran su nono yadda ya kamata domin haka na rage kashi 13 bisa 100 na mace-macen yara da ake fama da.

Adeole – Gabriel ta ce ta yi wannan kira ne ganin kashi 52 bisa 100 na cututtukan dake kama yara ‘yan kasa da shekara biyar na da nasaba da rashin shayar da su nonon uwa yadda ya kamata.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa kasa da kashi 24 bisa 100 na jarirai ne suke samun shayarwar uwayen su wato nono na tsawon watanni shida a kasa Najeriya.

Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya Chimay Thompson ya fadi haka, sannan ya kara da cewa rashin yin haka na daya daga cikin dalilin dake kara mace-macen yara da mata.

” Shayar da yaro ruwan nono zalla na tsawon watanni shida hanya ce dake taimaka wa wajen inganta lafiyar yaro da na uwa.” Inji Thompson.

Sai dai bincike ya nuna cewa haka ba shine yake faruwa ba a kasar nan domin miliyoyin mata basa juriyar shayar da ‘ya’yansu nono na wannan tsawon lokaci.

Ya ce bincike ya nuna cewa shayar da ‘ya’ya nono zalla na tsawon lokaci na taimakawa wajen bada tazarar iyali, rage kiba, kare mace da kamuwa da hawan jini, kara dankon zumunci tsakanin uwa da ‘da.

Share.

game da Author