Jami’in hulda da jama’a na rundunar sojojin Najeriya Sagir Musa ya bayyana cewa dakarun sojin sun ceto mutane 54 daga maboyar Boko Haram a jihar Barno.
Musa ya fadi haka ne a wata takarda da ya raba wa manema labarai.
Ya ce dakarun sojojin sun ceto wadannan mutane wanda a ciki akwai mata 29 da yara 25 a kauyukan Ma’allasuwa da Yaa-Munye.
” Da Boko Haram suka hango sojojin sai suka arce da gudu suka kyale wadannan mutane da suka yi garkuwa da su.
Musa ya kara da cewa sojojin sun kuma far wa yankin Damasak inda suka kona rumfuna da mota biyu na Boko Haram.
Bayan haka Musa yace sojojin sun kama wani dansanda mai sun Markus John PNo 383106 dauke da harsashai da bindiga daya.
Ya ce sojojin sun kama John a shingen su dake Njimtilo hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
” Mun ga harsashai 146 da bindiga daya a cikin wata jaka da yake rike da ita sannan bincike ya nuna cewa John na hanyar sa ta zuwa jihar Legas ne a lokacin da aka kama shi.
Daga nan Musa ya kara da cewa a wannan shingen dake Nijimtilo dakarun sojoji sun kama wasu sojoji biyu da Paul Ojochegbe mai lamba 14NA7113208 da Oko Eke mai dauke da lamba 12NA672586 dauke da bindiga daya kirar ‘AKA 47 Rifle’.
A karshe ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hada hannu da jami’an tsaro wajen yaki da aiyukkan bata gari ta hanyar tona asirin su a duk inda suke.