Lai Mohammed ya iya shirga karya – Atiku

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya bayyana zarge-zargen da gwamnatin tarayya ta yi masa a ta bakin Ministan Yada Labarai, cewa karairayi ne kawai na borin-kunya.

Atiku ya fito karara ya ce “Lai makaryaci ne.”

Atiku ya yi wannan raddi ne a kan zargin da Lai Mohammed ya yi cewa jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar su na kokarin kitsa zagon-kasa ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin zargin, Lai ya ce:

“Tun da ake siyasa a Najeriya, ba a taba samun lokacin da jam’iyyar Adawa da dan takarar shugabancin kasa suka rika yi wa gwamnati zagon-kasa ba, kamar yanzu da PDP da Atiku suka fadi zaben 2019.”

“PDP da dan takarar ta na shugaban kasa su na yin kokarin kan su ko na wasu ’yan kanzagin su domin yi wa Gwamnatin Buhari zagon-kasa ta hanyar ruruta wutar siyasa a kasar nan, tun bayan faduwar su zaben 2019.

“Su na ta kokarin ganin sun haddasa rudun da za su ga Najeriya ta zame wa sugaban kasa mai wahalar sassafa akalar ta, ta hanyar munanan kalaman da PDP ke yadawa da kuma bayanan rudu da suke saki kafin zabe da kuma bayan zaben 2019.”

A na sa martani, Atiku ya bayyana cewa: “Ai ba abin mamaki ba ne don wadannan kalamai na zargi sun fito daga bakin tantirin makaryaci kamar Lai, wanda Shugaba Buhari ya nada Ministan Yada Labarai.”

Atiku ya kuma bayyana Buhari a matsayin shugaba mai mulkin Fir’aunanci. Ya zargi Buhari da kokarin goga wa jam’iyyar adawa bakin fentin wai ta na shirya zagon-kasa.

“Mu na so mu san dalilin irin wannan gaggawar da Gwamnatin Muhammadu Buhari ke yi wajen ganin ta goga wa PDP da dan takarar ta, Atiku Abubakar kashin kaji wai ya na kokarin yi wa gwamnati zagon-kasa.”

Haka Atiku ya bayyana, a cikin wani raddi da kakakin yada labaran sa, Paul Ibe ya fitar.

Atiku ya ce babu mamaki don Lai Mohammed ya kantara karya, domin ta zame masa jiki, har ma ta kai a ranar 13 Ga Mayu, 2019, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce:

“Mutane irin su Lai Mohammed, Abba Kyari da Adamu Adamu sun nabba’a, sun natsu a cikin watan azumi. Amma ban tabbatar ko da gaske ba ne fa.”

“Mutumin da hatta wadanda suka dauke shi aiki sun san tantagaryar makaryaci ne, wanda hatta a cikin watan Ramadan zai kantara karya, to don me ma ’yan Najeriya za su yi mamakin wannan sabuwar karyar da ya kantara?

Da Atiku ya koma kan Buhari, ya ragargaje shi sosai, ya na cewa:

“Ta yaya mutumin da ya yi mulkin Fir’aunanci, mutumin da ya yi juyin mulki ya kifar da gwamnatin dimokradiyya, sannan ya rike shugaban da ya kifar a zuci, har bayan mutuwar sa ya na jin haushin sa, sannan wai shi ne zai ce Atiku na neman shirya masa makarkashiya?

Takardar ta ce Atiku mutum ne mai son zaman lafiya, domin kowa ya tabbatar a rayuwar sa ba a taba samun sa da laifin haddasa fitina ba.

Atiku ya ce hatta bayan rasuwar Shehu Shagari, Buhari bai daina kullatar sa ba, domin abin takaicin da Atiku ya ce Buhari ya yi a wurin ta’aziyyar Shagari, abin kunya da haushi ne matuka.

Atiku ya ce borin-kunya ne kawai Buhari da ’yan kanzagin gwamnatin sa ke yi, saboda sun ga cewa PDP ta dauko hanyar tona asirin zamba da magudin zaben da suka tafka a lokacin zaben 2019.

Share.

game da Author