Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya ragargaji jam’iyyar PDP da dantakarar ta na shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar.
Jiya Laraba Lai ya bayyana cewa idan ba a yi hattara ba, irin mummunar adawar da Atiku da PDP ke nunawa za ta iya zama bala’i a kasar nan.
Cikin jawabin da ya yi a wurin taron manema labarai, Lai ya zargi PDP da Atiku cewa su na kulla zagon-kasa a kan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Kadan daga cikin abin da takaradar da Lai ya karanta, wadda kuma ta zo hannun PREMIUM TIMES, ta furta cewa:
“Tun da ake siyasa a Najeriya, ba a taba samun lokacin da jam’iyyar Adawa da dan takarar shugabancin kasa suka rika rika yi wa gwamnati zagon-kasa ba, kamar yanzu da PDP da Atiku suka fadi zaben 2019.”
“PDP da dan takarar ta na shugaban kasa suna yin kokarin kan su ko na wasu ’yan kanzagin su domin yi wa Gwamnatin Buhari zagon-kasa ta hanyar ruruta wutar siyasa a kasar nan, tun bayan faduwar su zaben 2019.
“Su na ta kokarin ganin sun haddasa rudun da za su ga Najeriya ta zame wa sugaban kasa mai wahalar sassafa akalar ta, ta hanyar munanan kalaman da PDP ke yadawa da kuma bayanan rudu da suke saki kafin zabe da kuma bayan zaben 2019.
Idan ba a manta ba, jiya Laraba ne Lauyan Atiku da PDP, ya nemi Shugabar Kotun Daukaka Kara, kuma Shugabar Kotun Sauraren Kararrakun Zaben Shugaban Kasa, Zainab Bulkachuwa da ta sauka daga cikin kwamitin alkalan kotun, saboda mijin ta dan jam’iyyar APC ne.
Mohammed Bulkachuwa, mijin Zainab ya ci zabe a karkashin APC a matsayin sanata daga jihar Bauchi.
Tun a zaben fidda-gwani dai Yusuf Tugger ya yi zargin cewa an tafka magudi domin shi ne ya yi nasara ba Mohammed Bulkachuwa ba.
A lokacin Tugger ya rika shiga kafafen yada labarai ya na nuna kwafen takardun yadda aka yi ya tsere wa Bulkachuwa da yawn tulin kuri’u, amma duk da haka aka bayyana Bulkachuwa a matsayin wanda ya yi nasara.