Mafi yawan mutane kan zubar da ruwan kwakwa a dalilin rashin sanin amfanin sa a jikin mutum.
Masana amfanin ruwan kwakwa da likitoci sun yi kira ga mutane da su rika shan ruwan kwakwa saboda sindadororin inganta kiwon lafiya da gyara jiki da yake da shi.
Ga amfanin ruwan kwakwa.
1. Ruwan kwakwa na warkar da ciwon kai. Idan mutum ya sha a lokacin da ya ke ciwon kai zai rika samun sauki.
2. Yana kawar da cutar daji musamman dajin dake kama dubura da nono.
3. Yana kawar da cutar siga wato ‘Diabetes’
4. Ruwan kwakwa na kawar da ciwon kafa ( Sanyin Kashi) wato ‘Arthritis’
5. Yana kara karfin ido.
6. Yana kaifafa kwakwalwa.
7. Shan ruwan kwakwa na rage kiba a jiki.
8. Yana kara karfin gaban namiji.
9. Ruwan kwakwa na gyara fatar mutum.
10. Yana kara tsawon gashi.
11. Shan ruwan kwakwa na kare mutum daga kamuwa da cutar koda da huhu.
12. Yana hana tsufa da wuri.
Discussion about this post