Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Jihar Kaduna, ta ki amincewa da rokon da jam’iyyar PDP ta yi cewa a sake kirga kuri’un zaben gwamnan jihar Kaduna.
Kotun ta yi watsi da wannan roko a matsayin wanda ba shi da wata sahihiyar madogara.
Shugaban Kotun, Ibrahim Bako, ya zartas da cewa kotun na da wa’adin da aka dibar mata na kwanaki 180, wadanda a cikin su ne za ta tabbatar da cewa ta kammala dukkan shari’un korafe-korafen zabe.
Mai Shari’a Bako ya ce don haka ba zai yiwu a sake shigo da batun sake kidaya kuri’a ba, saboda babu wadataccen lokacin yin haka.
Kotun ta kuma ki amincewa da gyaran da masu shigar da kara, wato PDP ta nemi a yi na a sake kirga kuri’un kananan hukumomi 12 kacal.
PDP da Isa Ashiru sun maka APC, INEC da Gwamna El-Rufai a kotu, inda suke kalubalantar nasarar da INEC ta ce sun yi zaben gwamnan jihar.
A ranar 9 Ga Mayu ne PDP da dan takarar ta Isa Ashiru suka shigar da wannan bukata ta su a gaban kotu.
A ranar 25 Ga Maris kuma sai lauyan PDP da Isa Ashiru, wato babban lauya Emmanuel Ukala (SAN) ya shigar da takardar neman yi wa bukatar su gyara, inda ya tsaya kawai ga neman a sake kidaya kuri’un kananan hukumomi 12 kadai.
Wadanda ya nemi a sake kidayawa din su ne: Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu, Igabi, Birnin Gwari, Giwa, Zaria, Sabon Gari, Makarfi, Kudan, Kubau, Soba da kuma Ikara.
Dama kuma su ne kananan hukumomin da APC ta lashe da rata mai yawa.
An dage shari’ar zuwa ranar 15 Ga Yuni, domin ci gaba da sauraren hujjojin da PDP da Isa Ashiru suka gabatar wa kotu.