Daya daga cikin masu takarar Shugabancin Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa yadda shugabannin jam’iyyar APC suka nuna goyon baya ga dan takara daya, karya doka ne, karfa-karfa ce, kuma tsantsar rashin adalci ne karara ga sauran duk wani mai sha’awar tsayawa takara.
Yayin da Ndume ya ce shugabannin APC sun karya tsarin dimokradiyya, sai dai kuma ya kara jaddada karfin guiwar da ya ce ya ke da ita na yin nasara a zaben, duk kuwa da cewa shugabannin jam’iyyar APC ba shi su ke goyon baya ba, Ahmed Lawan suke goyon baya.
Sanatan ya ce APC ta karya dokar kasa, kuma ta yi rashin adalci, dalili kenan ya fito domin ya karya wannan rashin adalci da karfa-karfar da APC ke neman yi wa Majalisar Dattawa, inda aka maida dattawan wasu kananan yara.
Ndume wanda wannan ne zangon sa na uku da zai shiga a Majalisar Dattawa, tun can baya ya ce ba za su yarda a yi wa Majalisa dauki-dora ba, kuma ko an dora, za su kalubalanta, domin an kauce wa dimokradiyya kuma an karya abin da dokar kasa ta gindaya, cewa ta hanyar zabe ne kadai shugabannin majalisa za su iya hawa kan kujerar su.
“Abin da Shugaban Jam’iyya ke kokarin yi kuskure ne kuma karya doka ne karara. Ina ganin idan na fito na kalubalance shi, na ce ya karya doka, to abin da na yi kishi ne na nuna, ba bajirewa ga jam’iyya ba.”
Idan ba a manta ba, majalisa ta taba dakatar da Ndume tsawon watanni shida saboda goyon bayan da ya nuna cewa ya kamata Majalisar Dokoki ta amince da Magu a matsayin Shugaban EFCC.
Idan ba a manta ba, har yau Magu ya na matsayin shugaban riko ne, domin Majalisar Dattawa ba ta amince da shi ba. Shi kuma Buhari bai mika mata sunan wani ba.
An dakatar da Ndume tsawon wata shida saboda ya goyi bayan Buhari yayin da Majalisa ta ki amincewa da Magu.
Discussion about this post