Idan Har Gwamnati Ba Zata Iya Rike ‘Yan Npower Ba, Ya kamata Ta Kara Musu Lokaci, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Ribar duk wata gwamnatin kwarai shine samar da farin ciki a cikin yan kasa. Muna sa rai gwamnatin Najeriya ta kwarai ce.

Sanin kowa ne, samar da akin yi yana cikin manyan burikan gwaunati. Da talauci da rashin aikin yi tagwayen juna ne.

Idan gwamnati ta samar wa da matasa manufa, lallai zata samu kwanciyar hankali wajen samar da cigaba a lardin da take mulka.

Matasa sune suka fi yawa a Afrika, kuma wannan gagarumar kadara ce, don matashi kadara ce a kasa idan aka yi amfani dashi ta yadda ya dace.

A cikin arzikin kasa (Tangible and intangible resources), mutum yafi komai amfani tunda komai dan Adam yana iya sarrafashi idan har an bashi ilimi. Ko kimiya da fasaha bata kai mutum amfani ba. Inji Karl Marx.

Nayi imani da Allah, duk mai kishin Najeriya zai so matasan kasar su samu abun yi, hakan ne zai samar da zaman lafiya da manufa a kasar.

A sakamakon haka ne muke rokon yan siyasa da su goyi bayan tabbatar da matasan da suke cikin tsarin Npower don a rage talauci da fatara a cikin matasa.
Kada hassada tasa wasu su soki tsarin, shi komai na rayuwa rabo ne kuma layi yake bi. Watarana zai zo kanka idan har layin yana tafiya.

Dole ayi tunanin makomar wadanda suke cikin tsarin saboda yanzu sun saba da kudi idan aka sallemsu zasu shiga wani hali musamman wadanda Allah bai saka wa kudin nasu albarka ba. Wasu kuma sun yi aure, wasu kuma iyayensu suke ciyar wa da kudin.

Matasan da suke cikin tsarin idan Allah yaso zasu rayu har su dauki wasu aiki a kasansu. Dama hakan shine manufar fito da tsarin. Don haka a basu damar da zasu kasance hakan insha Allah.

Tsarin yayi tasiri matika wajen samar da aikin yi, da yawa daga cikin matasa sun samu abun yi, masu shaidar takardar diploma sun koma makaranta don karasa karatunsu. Wannan ma cigaba ne.

A cikin wadanda suke cikin tsarin akwai wadanda sun tsaya da kafarsu, wasu kuma kudin da suke karba ya hadu da bukatar rayuwa don haka babu maganar ajjesu don yin sana’a.

Misali, akwai wadanda suke neman lafiyar wata cuta da take damunsu. Wasu kuma sun samu nasibi sosai. A sakamakon haka ne muke bawa gwaunati shawara da ta kara zangon aikin idan har ba zata iya basu aikin din-din-din ba.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author