Tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ya koka kan yadda jabun magunguna suka karade kasar nan.
Abdulsalam ya fadi haka ne da yake ganawa da kungiyoyin NIPSS da DRPPS suka a gidansa dake Minna jihar Neja.
ABINDA ABDULSALAM YA CE
” An yi aiyukka da dama tun da aka kafa NIPSS sannan ina mai farin cikin yadda jagoran wannan tawaga ya fadi cewa a wannan shekara kungiyar zata tallafa wa gwamnati wajen tsaro hanyoyin da suka fi dacewa a samar wa mutane kiwon lafiya na gari.
” Tun a 1985 da nake cikin wannan kungiya, matsalar kiwon lafiya na cikin matsalolin da kungiyar ta maida hankali akai don ganin an inganta shi.
Abdulsalam ya ce a lokacin da yake NIPSS kungiyar ta yi fama da matsalar magunguna da lokaci aikin su a cika sannan kuma suna ajiye a dakunan ajiye magani dake jihar Filato. ” Akwana a tashi wasu har suna anfani da wadannin magani da basu da kyau.
” A zamanin mulkin soja ne NIPSS ta bankado wannan ma’ajiya sannan daga baya aka kona su duka.
Abdulsalam ya yi kira ga kungiyar da ta ci gaba da aikin sa ido kan jabun magunguna da magungunan da wa’adin aikin su ya cika.
” Addu’a na shine Allah ya kawo ranan da kungiyar NIPSS za ta rabu da matsalar rashin kudi da take fama da shi’’.
JABUN MAGUNGUNA
Bisa ga sakamakon binciken NOIPOLLS, kashi 18 bisa 100 na ‘yan Najeriya sun yi fama da jabun magunguna da kuma magungunan da lokuttan aikin su ya cika.
Idan ba a manta ba hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa (NAFDAC) ta bayyana cewa kashi 17 bisa 100 na magungunan dake kareda kasar nan jabu ne.
Discussion about this post