‘Yan ta-kifen Minista Ngige sun kife wakiliyar PREMIUM TIMES da ruwan duwatsu

0

’Yan jagaliya da ’yan iskan gari, masu goyon bayan Ministan Kwadago, Chris Ngige, sun yi wa wakiliyar PREMIUM TIMES rajamu da duwatsu da buraguzan kwalabe.

Ba ita kadai suka kai wa hari ba, sun kuma raunata wasu mambobin Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ’yan Kungiyar Kwadago ke zanga-zanga a kan hanyar kofar gidan Ngige, cikin unguwar Asokoro, Abuja.

Masu zanga-zangar dai duk ma’aikatan gwamnati ne, kuma suna zanga-zangar nuna fushin lattin daukar tsawon lokacin da aka yi ba a rantsar da hukumar gudanarwar wata hukumar da ke karkashin Ma’aikatar Kwadago da Ngige ke shugabanci ba.

’Yan jagaliyar Ngige sun yi taho-mu-gama da masu rera wakokin neman a biya musu bukatar su, wato a rantsar da Mambobin Hukumar NSITF, a kofar gidan Ngige, a Asokoro.

Dama kuma sun tare bangarori biyu na titin gidan da motocin ‘tanka’ yadda ba za a iya wucewa ba.

Wakiliyar PREMIUM TIMES, Adegboyega da ke daukar rahoton zanga-zangar, ta kasance ta na daukar rikodin na bidiyon duk abin da ke faruwa a kofar gidan, tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan iskan gari magoya bayan Minista Ngige.

Ta bayyana cewa an shafe kusan awa daya cur ana kafsawa tsakanin su, kuma ga ’yan sanda kusa da wurin, amma ba su shiga tsakani ba.

Daga nan sai ‘yan jagaliyar suka dirar wa wakiliyar PREMIUM TIMES da ruwan duwatsu da kwalabe, yadda tilas ta sheka a guje ta bar wurin.

Sai dai kuma uku daga cikin su, sun rufa ta a guje, suka kure mata gudu, suka kama ta, suka kwace duk abin da ke hannun ta.

“Sun rika mulmular min jiki, sannan suka kwace jaka ta, suka zazzage duk abin da ke ciki, suka dauke. Sun dauke min wayoyi guda biyu, da ‘yan kudin da ke ciki, da alabe da sauran tarkacen da ke cikin jaka ta.” Inji ta.

Adegboyega ta ce sai da ta sharara musu karya ta ce musu ta je unguwar ne neman aikatau ko wanke-wanke a gidajen manyan unguwar, sannan suka kyale ta.

Sauran ‘yan jaridar da ke wurin sun ce sun shaida biyu daga cikin ’yan jagaliyar, jami’an tsaron ofishin Ngige ne.

Ta ci gaba da cewa sai da wani ya ji tausayin ta, ya dauki naira 1,000 ya ba ta domin ta hau mota ta koma ofis.
Sannan ta ce a gaban ta aka ji wa direban Babban Sakataren NLC, Peter Ozo-Esan rauni.

Da yawa kuma daga mabobin Kungiyar Kwadago din an ji musu rauni tare da jibgar su da aka yi.

ASALIN RIKICIN

Asalin rikicin ya faro ne tun daga tankiyar da ta kaure tsakanin Kungiyar Kwadago, NLC da Ministan Kwadago, Chris Ngige, a kan rantsar da Mambobin Hukumar Gudanarwar NSITF, wadanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya nada, cikin Oktoba, 2017.

Su 11 amm har yau Ngige ya ki amincewa ya rantsar da su. Wannan ne ya haifar da kwatagwangwamar zanga-zanga har kofar gidan Ngige.

Shekara hudu kenan da cikar mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, amma har yau ba a rantsar da su sun kama aiki ba.

Share.

game da Author