Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman ya bada sanarwar cewa masarautar Katsina ta dage shagulgular sallah a wannan shekara.
Sallaman Katsina, Bello Ifu da ya saka wa takardar sakon hannu, yace sarki na juyayin rasa rayuka da akayi a dalilin hare-haren yan ta’adda da suka addabi wasu sassan jihar.
Ga sakon
” Mai martaba sarkin Katsina Alh. Dr Abdulmumini Kabir Usman CFR ya umarceni da in sanar da daukacin al’ummar jihar Katsina baki daya cewar bisa ga Ibtila’in da ya fadawa yanuwanmu na yankin gundumomin Batsari, Dan-Musa, Kankara da Wagina da dai sauran wuraren da abin ya shafa.
” Don haka masarautar ta yanke shawarar cewar ya zama wajibi ta dage hawan sallah da duk wani shagulgula na Sallah don nuna alhinin mu ga wadanda masifar ta shafa.
” Amma za’aje sallar Idi kamar yadda aka saba sannan za a gudanar da addu’o’in zaman lafiya. Muna rokon Allah subhanahu wata’ala ya zaunar da Katsina da ma kasar mu lafiya.
Idan ba a manta sarkin Katsina Abdulmumini ya koka kan yadda mahara suka addabi mutanen jihar. Ya aka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari sako cewa lallai a kawo wa jihar dauki maza-maza domin abin fa ya baci.