Ibadar I’itikafi A Kwanaki Goma Na Karshen Ramadana, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Ibadar I’itikafi A Kwanaki Goma Na Karshen Ramadana

Daga, Imam Murtadha Gusau

Asabar, Ramadan 20, 1440 AH (Mayu 25, 2019)

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Lallai dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakon sa, kuma muna neman gafarar sa. Kuma muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunan mu da munanan ayukkan mu. Wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, kuma wanda ya batar babu mai iya shiryar da shi. Kuma ina shaidawa lallai babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake, ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad (SAW) bawan sa ne kuma Manzon sa ne.

Bayan haka, ya ku ‘yan uwana Musulmi masu girma, masu daraja. Ya aka ji da Ibadah a cikin wannan wata na Ramadana mai albarka? Ina rokon Allah ya amsa muna, amin.

Yau kuma In Allah yaso zan yi dan takaitaccen tsokaci ne game da Ibadar I’itikafi. Ina fata, tare da rokon Allah ya datar da ni da abinda yake mafi daidai, amin.

Ya ku Musulmi! Ku sani, ma’anar I’itikafi a harshen larabci shine: lizimtar wani abu da tsare kai a kansa.

Sannan ma’anar I’itikafi a yare na shari’ah shine: Lizimtar dakin Allah, wato Masallaci don bauta wa Allah Madaukakin Sarki da neman kusanci zuwa ga re shi.

Sannan mu sani, I’itikafi yana daga cikin ayukka masu girma da falala, da biyayya ga Allah mai girma da daukaka. An karbo Hadisi daga Aisha – Allah ya yarda da ita – tace:

“Manzon Allah (SAW) ya kasance yana yin I’itikafi a kwana goma na karshe na watan Ramadana, har Allah ya karbi ransa.” [Bukhari ne ya rawaito]

Sannan shi Ibadar I’itikafi an shar’anta muna shi mu da wadanda suka gabace mu. Allah Madaukakin Sarki yace:

“Mun yi wasiyya ga Ibrahim da Isma’ila cewa su tsarkake daki na saboda masu Dawafi da I’itikafi da masu Ruku’i da Sujjadah.” [Suratul Bakarah: 125]

Kuma shi I’itikafi yin sa Sunnah ne a kowane lokaci, amma wanda yafi falala shine na goman karshe a cikin watan Ramadana, saboda Manzon Allah (SAW) ya dawwama a kan yin I’itikafin goman karshe na watan Ramadana. [Dubi Zadul Ma’ad]

Kuma Sharuddan I’itikafi sun hada da:

1. Niyyah

Mai I’itikafi zai yi niyyar lizimtar Masallaci don kusanci ga Allah da bauta masa. Saboda Manzon Allah (SAW) yace:

“Dukkan ayukka suna karbuwa ne da niyyah.” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

2. Masallacin da za ayi I’itikafi a cikin sa ya zamanto na Juma’ah ne.

Ma’ana ya zama Masallaci ne da ake yin Sallar Juma’ah a cikin sa, wato mutanen gari gaba daya suna taruwa a cikin sa. Ba Masallacin wata unguwa kadai ba.

3. Mai yin Ibadar I’itikafi ya zamanto yana da tsarki daga babban kari. Kamar janaba, haila, jinin biki da sauran su.

Domin I’itikafin mai janaba ba ya inganta, haka ma mai haila, da mai jinin biki, saboda wadannan ba ya halatta su zauna a Masallaci.

Sannan kasancewa da azumi ba Sharadi bane a I’itikafi:

Ba’a lissafa azumi a cikin sharuddan yin I’itikafi, saboda abin da aka ruwaito daga dan Umar – Allah ya yarda da shi – yace:

“Umar ya tambayi Manzon Allah (SAW) yace: “Na yi bakance a Jahiliyyah cewa zan yi I’itikafin dare daya a Masallacin Harami (Wato Makkah) sai Manzon Allah yace: “Ka cika bakancen ka.” [Bukhari ne ya rawaito shi]

Da ace yin azumi sharadi ne, da I’itikafin dare daya bai inganta ba, saboda ba’a yin azumi da daddare. Haka nan ya tabbata cewa:

“Manzon Allah (SAW) yayi I’itikafin goman farko na watan Shawwal.” [Muslim ne ya rawaito shi]

Sannan a cikin wadannan kwanaki na Shawwal kuwa akwai ranar Idi, wadda kamar yadda muka sani, ba ya halatta ayi azumi a cikin ta. Kuma kamar yadda muka sani, da azumi da I’itikafi kowane Ibadah ce mai zaman kanta, don haka babu sharadin sai an samu daya sannan dayan zai inganta.

Kuma lokacin fara I’itikafi da yin sa sananne ne. Ya inganta ayi I’itikafi a kowane lokaci, sai dai abin da yafi, kada I’itikafi ya gaza kwana daya, domin ba a samo daga Annabi (SAW) ba ko wani daga cikin Sahabban sa cewa yayi I’itikafin kasa da kwana daya.

I’itikafin kwana goman karshe a cikin watan Ramadana:

Wannan lokaci shi yafi dukkanin lokutan yin I’itikafi falala, saboda abinda ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – tace:

“Manzon Allah (SAW) ya kasance yana yin I’itikafin kwana goma na karshe a watan Ramadana, har Allah ya karbi ransa.” [Bukhari ne ya rawaito shi]

Kuma wanda yayi niyyar shiga I’itikafin goman karshe na watan Ramadana, sai yayi Sallar Asubah a wayewar garin ashirin da daya ga watan Ramadana, a Masallacin da yake so yayi I’itikafi a cikin sa.

An karbo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – tace:

“Manzon Allah (SAW) ya kasance yana yin I’itikafi a kowane wata na Ramadana. Idan yayi Sallar Asubah sai ya shiga wurin da zai yi I’itikafin a cikin sa.” [Bukhari ne ya rawaito shi]

Kuma I’itikafi yana karewa ne da faduwar ranar karshe daga Ramadana. Amma abin da yafi shine, a fita daga I’itikafin a wayewar ranar Idi, saboda shine abin da ya tabbata daga magabata (wato Salaf).

Kuma yana daga cikin hikimar yin I’itikafi itace yankewa daga barin duniya, da kaucewa shagalta da ita da ma’abotan ta, da kuma maida hankali ga Ibadah, da yin addu’a da kuma kai koke-koke da kai kara ga Allah Subhanahu wa ta’ala a kan matsalolin da suka dame mu, don haka ya dace ga mai I’itikafi ya shirya zuciyar sa domin hakan.

Abubuwan da suka halatta mai I’itikafi yayi sun hada da:

1. Fita daga cikin Masallaci saboda yin abin da ba makawa sai an yi shi, kamar fita don cin abinci da shan ruwa, idan babu wanda zai kawo masa su, da fita don biyan bukata (wato bayan gida ko fitsari).

Saboda abin da ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – tace:

“Manzon Allah (SAW) ya kasance idan yana I’itikafi yana kusanto min da kansa in taje masa shi, kuma ya kasance ba ya shigo wa gida sai don wata bukatar dan Adam.” [Muslim ne ya ruwaito shi]

2. Taje kai da gyara shi, saboda Hadisin da ya gabata.

3. Yin magana da mutane cikin abin da yake da amfani, da tambayar halin da mutane suke ciki, sai dai kada a yawaita hakan, saboda zai sabawa manufar I’itikafi.

4. ‘Yan uwa da makusanta su ziyarci mai yin I’itikafi, shi kuma ya fito don raka su. An karbo daga Safiyyah ‘yar Huyayy – Allah ya yarda da ita – tace:

“Manzon Allah (SAW) yana I’itikafi, sai nazo masa ziyara a wani dare, nayi magana da shi, sannan sai na tashi, don in tafi, sai ya tashi ya raka ni.” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

Abubuwan da suke bata I’itikafi sune kamar haka:

1. Barin Masallaci da gangan ba tare da wata bukata ba, koda kuwa na dan lokaci kadan ne.

Saboda abin da ya tabbata daga Aisha – Allah ya yarda da ita – tace:

“Manzon Allah (SAW) ya kasance ba ya shigo wa gida sai don wata bukatar dan Adam.” [Muslim ne ya rawaito shi]

Kuma saboda barin Masallaci ya sabawa zama a Masallaci, wanda rukuni ne na I’itikafi.

2. Saduwa da mace, koda kuwa da daddare ne.

Saboda fadin Allah Madaukakin Sarki:

“Kada ku rungumi matanku alhali kuna cikin I’itikafi a Masallaci.” [Suratul Baqarah: 187]

Kuma yana shiga cikin hukuncin saduwa, fitar da maniyyi tare da jin dadi, kamar yin wasa da hannu, da rungumar mace.

3. Yin niyyar yanke I’itikafi.

Idan Musulmi yayi niyyar I’itikafin wasu kwanaki kididdigaggu, amma sai ya yanke I’itikafin, to ya halatta ya rama shi, saboda abin da ya tabbata daga A’isha – Allah ya yarda da ita – tace:

“Manzon Allah (SAW) ya kasance idan zai yi I’itikafi, yana yin Sallar Asubah, sannan ya shiga wurin I’itikafin sa. Yayi umarni a kafa masa rumfa, yana so yayi I’itikafin goman karshe na Ramadana, sai matar sa Zainab tayi umarni a kafa mata rumfar ta, aka kafa mata, sauran matan Annabi (SAW) su ma suka yi umarni aka kafa masu rumfunan su. Da Manzon Allah (SAW) yayi Sallar Asubah, ya duba sai yaga an kafa rumfuna, sai yace, “aikin alheri kuke nufi?” Sai yayi umarni a cire rumfar sa, ya fasa yin I’itikafi a watan Ramadana, yayi I’itikafin a goman farko a cikin watan shawwal.” A wata ruwaya “goman karshe ma Shawwal.” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]

4. Mai I’itikafi ba ya zuwa duba marar lafiya, ba ya halartar jana’izah.

Abin da ake bukata shine, mai I’itikafi ya dukufa a kan bautawa Allah a wurin I’itikafin sa.

Wassalamu Alaikum,

Allah shine mafi sani.

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi Nigeria. Za’a iya samun Imam a wannan adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.

Share.

game da Author