Sanata Ali Ndume ya yi wa Majalisar Tarayya shigar farko tun a cikin 2003, a matsayin dan Dan Majalisar Tarayya, wanda yanzu kuma sanata ne a karo na uku.
Ndume wanda ya na daga cikin masu fafutikar ganin ya zama Shugaban Majalisar Dattawa nan da wata daya idan har an zabe shi, ya tattauna da PREMIUM TIMES, inda ya fadi dalilan da suka sa ya ke neman zama Shugaban Majalisar Dattawa.
PTH: Ana ji-ta-ji-tar cewa ku da ke takarar neman Shugaban Majalisar Dattawa ana matsa muku lamba ku janye wa mutum daya. Shin ina aka kwana batun takarar ka?
Ndume: To ni ma dai a shafukan jaridu ne kadai na ke ganin labarai wai ana matsa mani lambar na janye. Amma dai har yau din nan babu wanda ya zo ya ce min na janye, kuma ban taba cewa kowa ya janye min ba.
Saboda na san takarar zama shugaban majalisa hakkin kowane sanata ne, dokar kasa ce ta ba shi. Duk wanda ya ga zai iya, sai ya fito takara.
Bari na sake fadi, na shiga wannan takara bisa dalilai da yawa. Na farko dai an damka wannan shugabanci ga sanatocin Arewa maso Gabas, wadanda ina cikin su. Na biyu muka ina da yakinin cewa akwai gudummawar da zan iya bayarwa wajen sake saisaita shugabancin majalisar dattawa.
Dalili kenan ma jim kadan bayan na bayyana fitowa ta takara sai na fitar da kudirori na guda tara da zan shimfida mulkin majalisa a kan su.
PT: To amma kuma jam’iyyar ku ta rigaya ta tsaida wanda ta ke so ya zama shugaban majalisa. Ka na ganin ka na da yiwuwar samun nasara kuwa?
Ndume: Allah ke bada mulki ga wanda ya ke so kuma a lokacin da ya ga dama. Don haka idan Allah ya ce ni ne zan yi shugabancin majalisar dattawa, ita kuma jam’iyya ta ce ga wanda ta ke so, ai wanda Allah ya hukunta ne zai yi, ba wanda jam’iyya ke so ba.
Na biyu kuma shugaban jam’iyya ne ya tsaida shi ya ke so lallai shi zai zama shugaba. Amma ban san da batun Kwamitin Zartaswa ko Kwamitin Amintattun jam’iyya sun tsaida shi ba.
Sannan kuma na san dai a wurin taro an bada shawarar hakan. Don haka shawara kuma ba hukunci ba ne. Ina tuntubar Shugabannin Zartaswa da dama.
PT: Me ya sa ka ke ganin kai ne ya fi dacewa ka yi shugabancin?
Ndume: Ni fa ban ce na fi kowa cancanta ba. Amma dai ina daya daga cikin wadanda suka cancanta. Tun 2003 na ke a Majalisar Tarayya. Na yi shugabancin marasa rinjaye, sannan kuma na yi Shugabancin Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa.
Ka ga a yankin Jihar Barno Boko Haram ya kassara al’umma, ga talauci da sauran su akwai bukatar kara fito da tsare-tsaren da za su kara inganta yankin da Arewa maso Gabas gaba daya.
Kamar yadda na fada, ina da ajandoji har guda tara da za su amfani kasar nan baki daya ba wai wani yanki daya shi kadai ba
PT: Lokacin da shugaban jam’iyya ya fito ya ce sun tsaida wanda zai yi shugabancin majalisa, ka shiga jaridu a fusace ka na caccakar sa. Me ya sa ka yi wannan irin fushi haka?
Ndume: Zan iya cewa raina ya baci matuka saboda shugaban jam’iyya ya karya doka da tsarin mulkin Najeriya yace a bi idan za a zabi shugabannin Majalisar Tarayya. Ina wakiltar kananan hukumomi tara, sannan kuma ga shi na fito takara.
Na biyu kuma babu wanda ya tuntube ni ballantana a ce wai an tuntubi kowa. Ni ba karamin yaro ba ne. Shekaru na 60 a duniya.
NA TABA KADA AHMED LAWAN A ZABE AKA HANA NI -Ndume
Idan ana maganar biyayya ga jam’iyya, ai babu wanda ya fi ni biyayya. Saboda na taba kayar da shi a zaben Shugaban Masu Rinjaye a 2015, amma aka danne min hakki, aka ba shi. Kuma na dauki kaddara, na hakura.
Na biyu, daga cikin dukkan wadannan ‘yan takara na fi kowa bayar da gudummawar samun nasarar wannan jam’iyya. Zan iya bugun kirjin cewa na bayar da gudummawa sosai wajen samun nasarar wannan jam’iyya.
A lokacin zabe, ni ne aka nada Darakta Janar na Kamfen din Shugaban Kasa a yankin Arewa maso Gabas. Kuma na yi iyakar kokari na kawo wannan yanki.
Ire-iren mu da su Sanata Goje duk mun kawo nasarar jam’iyya kashi 100 bisa 100. Don haka mun cancanta jam’iyya ta karrama mu wajen tuntubar mu idan za ta tsaida wanda ta ke so ya yi shugabanci.
Ni dai ban san wadanda suke cewa wai sun tuntuba ba, domin dai ni da Sanata Goje ba a tuntube mu ba. Sannan har yanzu ni dai jam’iyya ba ta fito ta kira ni ta ce min ga wanda ta ke so ya zama shugaban majalisar Dattawa ba.
Na fada kuma zan sake fada, shi ma shugaban jam’iyya ai ba tilasta mana a ka yi sai shi za mu zaba ba, cimma matsayar dan takara daya aka yi. Kuma duk da an cimma matsayar, sai da muka kashe dare guda cur a Dandalin Eagle Square mu na zaben shugabanni.
Don haka duk wanda ke ta kumajin zuwa ya shirya wani abu da ya kauce wa dokar kundin tsarin mulki, ba za mu amince masa ba.
Na sha fada cewa da na bi gayyar-sodi, gara na tsaya ni kadai, idan ma an kayar da ni, shikenan. Ballantana kuma ina da dimbin magoya baya a ciki da wajen majalisa.
Ni ban ce Goje ko Ahmed Lawan su janye min ba. Idan ma har zan iya yin haka, to ni ne zan nemi ta haka, ta hanyar amincewar juna. Ba wai haka kawai wani ya je yace musu su janye min ba.
PT: Ba ka ganin cewa ko suna tsoron ba zaka bauta wa jam’iyya yadda ya kamata ba kuma ba za ka yi mata biyayya ba, shi ya sa suke nemen dora wani ba kai ba?
BABU SANATAN DA YA FI NI BIYAYYA GA JAM’IYYA -Ndume
NDUME: Idan ana maganar biyayya, ai na dade ina yi wa jam’iyya biyayya. Haka kuma ina cikin wadanda suka dade a cikin guguwar Buhariyya. Tun cikin 2002 na shiga kungiyar Goyon Bayan Buhari (TBO). Daga nan nayi APP, nayi ANPP. Da Buhari ya koma CPC ni kuma na koma PDP. Kusan ma shi ne dalilin komawa ta APC.
Don haka ina ma ganin idan ana neman wadanda suka dade su na bauta wa jam’iyya da kuma goyon bayan Buhari to tilas a sa da ni.
Na jajirce na goyi bayan Buhari a 2015, inda na ce lallai ya kamata a nada Magu, yayin da Shugabannin Majalisa su kuma ba su yarda mu goyin bayan amincewa a nada magu a matsayin Shugaban EFCC na dindindin ba. wannan ya janyo min har dakatar da ni aka yi na tsawon watanni shida daga majalisa.
An tilasta min na bi gayyar-sodi kamar yadda sauran dattawan majalisa suka yi, amma na ki amincewa da ra’ayin su.
Ina tabbatar wa kowa cewa abin da shugaban jam’iyya ke son yi kuskure ne kuma karya doka ne.
Idan ya yi haka ya karya ‘yancin dimokradiyya. Ya kamata tun da wuri ma su canja shawara. Domin hatta Kotun Koli kan canja hukunci idan daga baya ta gano cewa ta tabka kuskure a wata shari’ar da ta yanke hukunci a baya.