Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Tukur Buratai, ya kara jaddada cewa tuni sojoji suka murkushe Boko Haram, suka kakkabe su.
Ya ce wadanda ake yaki da su a yanzu, gungun rikakkun mamyan ‘Boko Haram’ din kungiyar ISWAP ne masu ganin sai sun kafa kafa shari’ar musulunci a Afrika ta yamma.
Buratai ya ce abin da ke faruwa yanzu a Arewa maso gabas, maharan kungiyar ISWAP ne da suka zama rikakkun mabarnata a duniya, suka yi ambaliya a yankunan can ciki, suka karya doka tare da hare-hare a jihohi makwabta na bangaren Afrika ta Yamma.
Buratai ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da wasu yara dalibai suka kai masa ziyara, domin su koyi darasi daga wani littafi da aka buga a kan tarihin Buratai.
Sunan Littafin ‘The Legend of Buratai’, wanda tun a ranar 17 Ga Mayu aka kaddamar da shi.
“Farkon abin da na fara yi bayan an nada ni, sai na kira Daraktan Yada Labarai na ce masa ina so duk wani abin da sojoji suka yi, to a sanar a kafafen yada labarai, kowa ya san irin ayyukan da muke yi.
“Jama’a na da ‘yancin sanin abin da muke yi. Saboda sojojin na su ne, wato na Najeriya. Bai kamata a rika samun gibin sanar da bayanan ayyukan da sojojin mu ke yi a Arewa maso Gabas ba.
“A baya mun sha cin karo da matsalar masu bada labarai na karya sabanin abin da ke faruwa, domin su kashe wa sojojin mu guiwa.
“Ganin haka sai muka fara bada rahotannin abin da ke faruwa a wuraren yaki a Arewa maso Gabas, ba tare da an yi karin gishirin karairayin komai ba.
“Sannan kuma mun sha fama da Kungiyoyin Agaji na Kasa da Kasa, ciki har da Amnesty International, wadanda ba su ganin kokarin mu sai laifin duk wani abin da muka yi.
“Na yi amanna su na da da wata boyayyar manufar da suka maida hankali suna bada rahotannin karairayi a kan sojojin Najeriya. Duk da haka amma mu na kafa kwamitin bincike, kuma sai mu gano zargin da suke yi mana duk karairayi ne.
“Saboda mu na tabbatar da cewa duk wani aiki da sojoji za su yi, to sun yi shi ne kamar yadda dokar a-fita-a-fafata ta gindaya.”
Buratai ya ce babban karfin halin sojoji shi ne taken su na: “Ba gudu, ba ja dabaya, kuma banda sadanda”.
Dalibai daga makarantu da dama ne suka kai ziyarar, ciki har da White Plain British Schools, Abuja, Gifted Hunira Arcade da sauran su.
Discussion about this post